Sabuwar doka a Kaduna: Bulala 7 da kuma tarar N200 ga duk masu fitsari ko kashi a waje
- Jikin masu kunnan kashi zai fada musu domin wata sabuwar doka da aka sanya ajihar Kaduna
- Sanya dokar dai ya biyo bayan yawaitar kashi da fitsari a ko'ina da mutane suke yi
A yunkurin tabbatar da tsaftar muhalli domin kaucewa yaduwar cututtuka, yanzu haka yin kashi ko fitsari a fili ya zama laifi inda hukuncin bulala 7 da kuma tarar Naira 200 ya hau kan duk wanda yayi a unguwar Damaru dake karamar hukumar Soba ta jihar Kaduna.
Shugaban kwamitin tabbatar da tsaftar muhalli na yankin Malam Adda’u Ibrahim ne ya tabbatar da hakan sannan duk wanda ya aikata laifin, zai wanke sannan ya goge wurin da ya bata sosai kamar yadda yake ada.
Ibrahim ya shaida hakan ne ga wakilin kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a yau Alhamis yayin da suke bitar irin nasarorin da shirin tabbatar da tsaftar muhallin karo na II na kasa baki daya mai taken (SHAWN) ya haifar.
Ya ce sun dauki wannan mataki ne domin kawo karshen dabi’ar yin hutu a waje da kuma yunkurinsu na farfado da dabi’ar tsafta a tsakanin mutane don magance barkewar cututtuka.
“Kafin sanya wannan doka abu ne mai sauki kaga kowa na kashi ko fitsari a duk inda ya ga dama musamman yara kanana, wanda kuma da ruwan saman yazo sai ya koro shi cikin rijiyoyinmu tare da duk wani datti.
Kuma kasancewar ba mu da wani zabi haka muke wanka da girki har ma mu sha, wanda kuma hakan ke haddasa yaduwar cututtuka da kuma barkewar amai da gudawa” ya bayyana.
Amma ya ce labarin yawaitar ziyar asibiti don neman magani da mazauna yankin suke ya ragu tun bayan da aka zabi yankin nasu a tsarin tsaftar muhalli na SHAWN II a shekara ta 2017.
Ya kuma kara da cewa tsarin ya taimaka musu wajen karfafa musu gina bandakuna a gidajensu da ma wanda sauran mutane zasu na amfani da shi gami da samar musu da hanyoyin samun ruwan sha mai tsafta daga birtsatsai.
KU KARANTA: Ayya: Wasu ‘yan sanda 2 da wasu mutane uku sun sheka lahira a jihar Rivers
Mariya Abubakar ‘yar shekara 13 da majiyarmu ta zanta da ita yayin da take diban ruwa a daya daga cikin birtsatsan da aka samar musu, ta bayyana cewa yanzu a dalilin samun ruwa kusa tana samun lokaci isasshe na yin karatu da kuma wasa.
Mai unguwar kauyen Alhaji Gambo Yusuf ya godewa gwamnatin jihar Kaduna da kungiyar UNICEF da kuma DFID bisa ceto rayuwarsu daga kangin rashin sani da kuma kayan habaka rayuwar mutanen yankin.
Kamfanin dillancin labarai ya rawaito cewa tsarin an samar da shi ne don habaka rayuwar al’ummar karkara ta hanyar tabbatar da tsaftar muhalli da dakile ba haya da fitsari a fili tare da nusar da mutanen yankin amfanin wanke hannu da samar da ruwan sha da kuma tsaftar jiki baki daya.
Gwamnatin kasar Birtaniya ce dai da sashin cigaban kasashen duniya da kuma kungiyar tallafawa yara ta majalisar dinkin duniya ce suke samar da kudaden aiwatar da aikin ga jahohin Kaduna, Katsina, Zamfara, Benue, Bauchi da kuma Jigawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng