R-APC ba kungiyar adawar jam’iyyar mu ba ce - APC

R-APC ba kungiyar adawar jam’iyyar mu ba ce - APC

Mallam Bolaji Abdullahi, babban sakataren labarai na jam’iyyar All Progressives Congress yace kungiyar sabuwar APC (R-APC) ba kungiyar adawar jam’iyya mai mulki ba ce ya kara da cewa har yanzu APC na nan a hade karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Abdullahi yace kungiyar R-APC sun yi maja da jam’iyyun adawa gabannin zaben 2019.

A cewarsa: “Muna girmama yancin kowa na shiga duk kungiyar da yake so don haka, muna son sanar da cewa kungiyar da ake kira da R-APC ba kungiyar adawar jam’iyyarmu bace. Jam’iyyarmu APC na nan a hade karkashin jagorancin shugabankasarmu Muhammadu Buhari.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Alhaji Buba Galadima, shugaban kungiyar sabuwar APC (R-APC) ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari da ajiye kudirinsa na sake takara a 2019 saboda zai sha kashi.

R-APC ba kungiyar adawar jam’iyyar mu ba ce - APC

R-APC ba kungiyar adawar jam’iyyar mu ba ce - APC

Galadima, wadda kungiyarsa ta R-APC ta hade da sauran jam’iyyun siyasa a ranar Litinin, 9 ga watan Yuli, yace Allah ya kaddata cewa shugaba Buhari zai fadi a zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Bana tunanin sabuwar jam’iyyar da PDP ta kafa zata iya tunkudar da jam’iyya mai mulki – Balarabe Musa

Ya kuma yi zargin cewa mambobin kungiyar siyasar sa na fuskantar barzanar mutuwa tunda suka bar APC ta hanyar sakonni.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel