NNPC ta shiga chakwakiya: Majalisa zata binciki Naira N100b da ba’a saka a asusun gwamnati ba

NNPC ta shiga chakwakiya: Majalisa zata binciki Naira N100b da ba’a saka a asusun gwamnati ba

- Bayan na neman haihuwa a kamfanin NNPC

- Ana zarginsu da rashin sanya wasu makudan kudade asusun gwamnatin tarayya

- Ko a watannin baya ma NNPC ta shiga wani zaman doya da manja tsakanin manyan shugabanninta

Majalisar dokoki ta kasa ta kaddamar da wani bincike da za ta gudanar akan Babban kamfanin mai na Kasa wato NNPC akan irin kudaden da ya samu a cikin shekarar nan.

NNPC ta shiga chakwakiya: Majalisa zata binciki Naira N100b da ba’a saka a asusun gwamnati ba
NNPC ta shiga chakwakiya: Majalisa zata binciki Naira N100b da ba’a saka a asusun gwamnati ba

Majalisar ta bayyana cewa dalilin ta na gudanar da wannan bincike shi ne irin yadda ake gudanar hada-hadar mai a kamfanin na NNPC wanda ya ke mallakar gwamnati

Binciken dai zai gano adadin yawan kudin da kamfanin ya samu a cikin shekarar nan da kuma hadin gwiwar da kamfanin ya ke yi, da kuma yadda fasalin rabon kudin da aka samu daga ribar mai ya ke gudana.

Haka nan Majalisar za ta kara duba yadda lamarin sayar da danyen man da ake ta hanyar sayar da shi akan kudin Dala, amma kuma sai kamfanin yake sakawa gwamnati Naira a maimakon Dalar.

KU KARANTA: Hadakarmu da PDP ba maja ce ba – Shugaban jam’iyyar APP

Daukar matakin kaddamar da binciken ya biyo bayan gabatar da wani kudiri da dan Majalisa daga jihar Delta na jamiyyar PDP mai suna Nicholas Ossai ya gabatar, inda ya ce rashin saka Naira biliyan 100 a asusun gwamnatin tarayyar da kamfanin bai yi ba, ya haifarwa da wasu jahohi da kananan hukumomi wadanda su ka dogara akan rabon kasafin arzikin kasa shiga cikin matsalar rashin biyan ma'aikata albashinsu na watan Yuni.

"Wannann al'amarin na gaza sakawa gwamnati kudin da ya kai Naira biliyan 100 da kamfanin mai na NNPC ya yi bai kamata ba, domin kuwa yanzu haka farashin danyen mai a duniya ya yi tashin gwauron zabi.

Idan aka bar irin haka ta cigaba da faruwa babu shakka akwai lokacin da kamfanin zai zama bai saka ko komai ba, wanda hakan ka iya jefa kasar nan wani hali na damuwa" In Ji Nicholas

Shi ma a nasa bangaren wani dan majalisa daga jihar Enugu dan jamiyyar PDP Dennis Amadi, ya bayyana takaicinsa akan yadda kamfanin mai na NNPC yake wasa da arzikin kasar nan, domin tun da farko an zargi shugabancin kamfanin da gudanar da harkokin kamfanin ta hanyar da bata dace ba, wacce kuma ba ta kan ka'ida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng