Fallasa: Dubun wasu 'yan madigo na daf da cika a jihar Kano

Fallasa: Dubun wasu 'yan madigo na daf da cika a jihar Kano

Hukumar nan ta gyaran da'a da tabbatar da tarbiyya ta jihar Kano a karkashin jagorancin babban malamin nan na addini, Sheikh Malam Aminu Daurawa ta sha alwashin kaddamar da binciken kwakwaf don gano ainihin gaskiyar faifan sautin wasu 'yan madigo da ya watsu a kafar sadarwar zamani a jihar.

Majiyar mu dai ta Daily Nigerian ra ruwaito cewa faifan sautin dauke da munanan kalaman batsa na wasu 'yan mata ne dai aka yi ta yamadidi da shi musamman ma kafafen sadarwar zamani a ciki da wajen jihar.

Fallasa: Dubun wasu 'yan madigo na daf da cika a jihar Kano
Fallasa: Dubun wasu 'yan madigo na daf da cika a jihar Kano

KU KARANTA: Saudiyya ta hana yan kasar Qatar aikin hajji

Legit.ng ta samu cewa sai dai kwamandan Hisbar da ke da alhakin binciken laifuka Alhaji Idris Ibn-Umar ya bayar da tabbacin cewa hukumar za ta binciki lamarin kuma zata hukunta duk wadda ta samu da laifi.

A wani labarin kuma, Mahukunta a hukumar rukunin kamfanonin da ke kula da albarkatun man fetur da iskar gas na kasa watau Nigerian National Petroleum Corporation, NNPC a takaice a ranar Litinin din da ta gabata sun sa hannu a wata yar jejeniyar gina matatar iskar gas bakwai.

Kamar yadda muka samu, idan aka kammala matatun iskan gas din, za su rika samar da iskan da ya kai ma'aunin iskar biliyan 3.5 a kullum wanda kuma ana sa ran kammala hakan ne zuwa shekarar 2020.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng