INEC zata daina rijistar katin zabe, ta bayyana dalilinta

INEC zata daina rijistar katin zabe, ta bayyana dalilinta

- A kokarin hukumar INEC na samarwa da jama'a katin jefa kuri'arsu, za ta dakatar da rijistar domin tattara bayanai

- Sai wanda ya mallaki katin zaben ne dai yake da damar jefa kuri'a a zabe mai zuwa na 2019

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bayyana dakatar da aikin rijistar zabe na wucin gadi. Hukumar ta bayyana cewa dakatawar zata fara ne daga ranar 17 ga watan Agusta, wanda hakan zai ba su cikakkiyar damar tattara bayanan mutanen da su ka yiwa tare kuma da samar musu katin jefa kuri’ar na dindin

INEC zata daina rijistar katin zabe, ta bayyana dalilinta
INEC zata daina rijistar katin zabe, ta bayyana dalilinta

Babban Sakataren hukumar ne Augusta Ogakwu ne ya bayyana haka cikin wata takarda da ya aikewa kwamishinonin hukumar. Ya kara da cewa matakin da su ka dauka ya biyo bayan tataunawa da masu ruwa da tsaki akan harkar.

KU KARANTA: Saboda tsananin hidimtawa Buhari da nayi, sau 38 ana kulle ni – Buba Galadima

"Masu ruwa da tsaki sun bayyana gamsuwarsu akan yadda hukumar ta mayar da hankali wajen ganin ta tabbatar da zaben 2019 mai inganci, kuma sun bukaci hukumar ta INEC da ta cigaba da dukkanin wani kokari da zai tabbatar da samuwar karbabben zabe" In ji Augusta Ogakwu.

A karshe ya tabbatar da cewa da zarar hukumar ta kammala samar da katin zaben na din-din zata sanar da al'umma domin su zo su karbi abinsu.

Enter headline

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng