Yadda za a shawo karshen rikicin Shugaba Buhari da ‘Yan Majalisa – Shehi Sani

Yadda za a shawo karshen rikicin Shugaba Buhari da ‘Yan Majalisa – Shehi Sani

Mun samu labari cewa Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu Sani ya bayyana yadda za a bi a magance wutar rikicin da ke tsakanin Fadar Shugaban kasa da kuma ‘Yan Majalisar Tarayyar kasar.

Yadda za a shawo karshen rikicin Shugaba Buhari da ‘Yan Majalisa – Shehi Sani
'Dan Majalisar Kaduna Shehi Sani tare da Buhari

Sanata Shehu Sani ya bada shawarar yadda za a zauna lafiya tsakanin manyan bangarorin na Gwamnatin Tarayya ne a wani dogon rubutu da yayi a shafin sa na Facebook kwanan nan. Sanatan ya bada shawara a daina batawa ‘Yan Majalisa suna.

Bayan nan kuma Sanatan yayi kira da masu rike da madafan ikon da su daina amfani da karfin mulki wajen taso keyar ‘Yan Majalisa a gaba. Shehu Sani ya kuma nemi wadanda Shugaban kasa ya ba mukami su rika ba Majalisa girman ta.

KU KARANTA: 2019: Sanatoci da manyan 'yan siyasa sun shigo Kaduna

‘Dan Majalisan Tarayya da ke wakiltar Kaduna a Majalisar Dattawa yace banbancin siyasa ne ya sa aka taso wasu Sanatoci a gaban Kotu. Sanatan ya kuma nemi Majalisar kasar ta tantance wadanda Shugaban kasa Buhari ya ba mukamai.

Bayan nan, Fitacccen Sanatan na Jam’iyyar APC ya nemi a ajiye maganr tsige Shugaban kasa Buhari sannan kuma a sa hannu a kan kudirorin da ya kawo gaban Majalisar. Sanatan yace dole kuma a ba Shugaba Buhari girman sa na Shugaba.

Kwanaki kun ji cewa Gwamnatin Buhari za ta karbe dukiyoyin wasu tsofaffin Gwamnoni da Ministoci a Najeriya da ake zargi da sata. Kudin da su ka samu ta sata za su koma hannun Gwamnati.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: