Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un: Wannan Amarya ta rasu a daren ranan aurenta

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un: Wannan Amarya ta rasu a daren ranan aurenta

Budurwa yar kasar Misra mai suna Samah ta riga mu gidan gaskiya a daren ranan aurenta bayanan kaita gidan mijinta.

Samah dai yar shekara 17 ce da haihuwa kuma rahoto ya nuna cewa ta rasu ne sakamakon ciwon zuciya da ya kamata bagtatan.

Yan garinsu da ke wani kauye kusa da jihar Al Dohliqiya sun samu wannan labari ne bayan an kaita gidan mijinta.

Jami’an yan sandan kasar sun gudanar da bincike kan sabon angonta, Mahmoud, dan shekara 28 da haihuwa kan abinda ya faru.

Amma bisa ga abinda ya bayyana har yanzu, ciwon zuciya ne ya kamata kuma yayi ajalinta.

Sabon Ango, Mahmoud, ya bayyanawa hukuma cewa amaryar Samah ta kasance bata jin dadi kafin ranan daurin auren. Ya ce a ranan daurin auren ma bata ci komai ba saboda tana fama da mugun ciwon ciki.

KU KARANTA: Zafin kishi ya sanya wata matar basarake kashe ‘yar kishiyarta

Amma aka bata magani wanda ya taimaka wajen samun sauki har akayi bikin auren cikin annashwa.

Wannan bas hi bane karo na farko da irin wannan abu zai faru a kasar Misra ba. Kwanakin baya wata yar shekara 22 ma ta rasu yayinda ake cikin bikin daurin aurenta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng