Kwankwaso ya yi ganawar sirri da mataimakin gwamnan jihar Kano a Landan (hotuna)
Kwankwaso ya yi ganawar sirri da mataimakin gwamnan jihar Kano a birnin Landan.
Tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai wakiltar yankin Kano ta tsakiya Rabi'u Musa Kwankwaso, yayi wata ganawar sirri da mataimakin gwamnan jihar Kano Farfesa Hafiz Abdallah a birnin Landan.
Zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani game da abubuwan da suka tattauna sai dai ana hasashen ganarwa tasu na da nasaba da siyasa.
Ga hotunan ganawar tasu:
KU KARANTA KUMA:
A baya Legit.ng ta rahoto cewa, A ranar Laraba, 5 ga watan Yuli ne wasu gugun matasan Kwankwasiyya suka shirya gangamin sanar da ficewarsu daga tafiyar jagoransu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da babbaka jajayen hulunansu gaba daya.
KU KARANTA KUMA: Hadimin Buhari ya gargadi dan majalisar wakilai kan kiran shugaban Najeriya da ya yi da azzalumi
A yayin wannan gangami na wadannan tsofaffin yayan halaliyar tafiyar Kwankwasiyya sun sauya ma tsohuwar tafiyar tasu kirari, inda suka ce ta koma ‘Kwankwasiyya wahala’ daga ‘Kwankwasiyya Amana”.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng