Da duminsa: Shugaba Buhari ya dira jihar Borno
Labarin da ke shigowa da dumi-dumi na nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari ya isa garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno a yau Juma'a. 6 ga watan Yuli, 2018.
Shugaban kasa ya tafi jihar Borno ne domin halartan taron zagayowar ranan sojin Najeriya wanda za'ayi a Monguno, jihar Borno.
Legit.ng ta samu wannan labari ne daga bakin gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, inda ya bayyana cewa:
"Da safen nan, na karbi bakuncin shugaba Muhammadu Buhari, a barikin sojin saman Najeriya dake Maiduguri."
Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Borno a yau Juma'a. Gabanin zuwansa, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya rigayesa da zuwa jihar Borno a jiya domin ganewa idonsa yadda ake shirye-shriyen bikin da kuma ziyara ga yan sansanin gudun hijra a jihar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng