Wani Jami'in karbar haraji ya kashe wani magini ta hanyar amfani da Zoben tsafi

Wani Jami'in karbar haraji ya kashe wani magini ta hanyar amfani da Zoben tsafi

- Aamfani da zaoben sihiri ya kar wani mai sana'ar gini lahira

- Lamarin y afaru ne sakamakon kin biyan haraji da yayi

- Nan take mai karbar harajin yayi amfani da zoben wajen kashe shi

A ranar larabar nan ne aka samu rudani a unguwar Ijaiye da ke birnin Abeokuta, bayan da wani mai karbar haraji mai suna Gbangba, ya zama ajalin wani magini mai suna Ibrahim Raji ta hanyar amfani da wani zoben sihiri.

Wani Jami'in karbar haraji ya kashe wani magini ta hanyar amfani da Zoben tsafi
Wani Jami'in karbar haraji ya kashe wani magini ta hanyar amfani da Zoben tsafi

Wannann Al'amarin ya faru ne a lokacin da maginin ya ke kan hanyarsa ta zuwa gurin aiki akan babur dinsa, inda mai karbar harajin ya bukaci da ya biya kudin haraji Naira 400, wanda shi kuma ya ce shi babur dinsa ba na haya bane.

Wani wanda ya ga yadda abin ya faru mai suna Emmanuel Dosunmu, ya bayyana yadda al'amarin ya faru.

KU KARANTA: Hatsaniya ta barke a garin Pankshin lokacin da Jami'an hukumar NDLEA su ke kokarin Cafke wani dillalin Kwaya

"Ibrahim Raji ya kasance mai gidana, kuma a jiya yayi min waya akan in shirya washegari domin zamu je aiki. Jim kadan da fitowarsa ne, ya hadu da malaman karbar haraji, wanda su ka bukaci da ya biya kudin haraji Naira 400. Shi kuma ya gaya musu, shi ba haya ya ke ba, wanda shi kuma mai karbar harajin ya nuna shi da wani zoben sihiri da ke yatsansa" in ji Emmanuel.

Faruwar wannan al'amarin ke da wuya, sai gungun masu haya da babur su ka gudanar da wata zanga-zanga a ofishin rundunar yan sanda ta Ibara, inda suka bukaci da a soke biyan harajin.

Kawo yanzu dai mamacin yana dakin ajiye gawarwaki da ke cibiyar kula da lafiya ta gwamnatin tarayya da ke Abeokuta. Yayin da shi kuma wanda ya aikata laifin yana tsare a hannun ‘yan sanda domin zurfafa bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng