Sojojin ruwan Najeriya sunyi nasarar lalata haramtattun matatun man fetir har guda 1500

Sojojin ruwan Najeriya sunyi nasarar lalata haramtattun matatun man fetir har guda 1500

- Sojin ruwa sunyi nasarar gamawa da matatun man da basu da lasisi

- Matatun da yawansu ya kai 1500 a jiha guda

Kimanin watanni biyu kenan wani jirgin ruwan yaki mallakin sojojin ruwan kasar nan ya lalata wasu haramtattun matatun mai wanda su ke ba bisa ka'ida ba, harguda 1500 a yankin jihar Delta.

Sojojin ruwan Najeriya sunyi nasarar lalata haramtattun matatun man fetir har guda 1500
Sojojin ruwan Najeriya sunyi nasarar lalata haramtattun matatun man fetir har guda 1500

Babban kwamandan jirgin kwamodo Ibrahim Dewu ne ya bayyanawa manema labarai hakan a yau din nan a birnin Warrin jihar Delta.

Babban kwamandan ya bayyana yadda suka aiwatar da aikin lalatarwar a yankin gabar ruwa ta Otumara da Ogbegugu da kuma Okpuku da ke Warri.

Ya kara da cewa jami'an rundunar yanzu haka suna tsibirin Bennett da ke karamar hukumar Warri ta Kudu, domin cigaba da wannan aikin.

KU KARANTA: Masu garkuwa da mutane sun sace mutane 2 a Kaduna

Sannan ya bayyana cewa masu haramtacciyar masana’antar sunyi iyakar kokarinsu na hana wannan aikin lalatarwar, ta hanyar sanya shinge, da kuma kunna wuta a kewayen gurin, amma sai dai duk da wannan bai hana su tabbatar da aikin da ya rataya a wuyansu ba.

Daga karshe ya ce kafa matatun mai ba bisa ka'ida ba yana kara kawo gurbacewar muhalli.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng