Yan sanda sun kama kansila kan kashe-kashen Benue

Yan sanda sun kama kansila kan kashe-kashen Benue

Rundunar yan sandan Najeriya ta kama wasu mutane takwas dake da alaka da kashe-kashen kwanan nan da ake yi a jihar Benue.

Jimoh Moshood, kakakin yan sanda, ya bayyana daya daga cikin wadanda aka kama a matsayin Benjamin Tivfa, kansilan mazabar Fidi a jihar.

A wannan shekarar kadai an kashe mutane da dama a jihar Benue.

A wata sanarwa da ya saki a ranar Talata, Moshood ya ce kansilan ya karbi bakin cewa ya baiwa wasu yan fashi makamai da alburusai domin aiwatar da miyagun ayyukansu.

Yan sanda sun kama kansila kan kashe-kashen Benue
Yan sanda sun kama kansila kan kashe-kashen Benue

Kakakin yan sandan ya lissafa sunayen sauran a matsayin Victor Ganabe (dan asalin garin Naka), Daniel Kyase (Mbaku), Adajo Tomza (Tse Egbe), Msugh Sengv (Naikpe).

Sauran su ne Julius Avaan (Ikpayongu), Terkula Udeh (Gwer West), Sunday Cheche (Guma).

KU KARANTA KUMA: Muna maraba da dawowar yan sabuwar PDP - Lamido

Ya ce sauran masu laifin da aka kama a ranar 27 ga watan Yuni, sun karbi bakin cewa su masu gadin dabbobi na jihar Benue ne.

Ya ce ana gudanar da bincike sannan za’a mika su kotu da zaran an kammala.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng