Bayan tabbatar da mutuwar wata mata kwatsam sai ga ta da ranta a cikin akwatin gawa a mutuware

Bayan tabbatar da mutuwar wata mata kwatsam sai ga ta da ranta a cikin akwatin gawa a mutuware

- Ashe da kwananta a gaba bayan wani mummunan hatsari ya rutsa da ita

- Duk kuwa da cewa likitoci bayan gwaje-gwaje sun tabbatar da mutuwarta

- Mai gadin dakin ajiye gawawwaki ne ya gano tana raye sannan ya ankarar da likitocin asibitin

Wata mata yar kasar Afirka ta kudu wacce aka bayyana mutuwarta sakamakon afkuwar wani mummunan hatsari da ya rutsa da ita, sai ga shi da ranta a dakin ajiye gawarwaki cikin wata na'urar sanyin da ake ajiye gawawwaki.

Bayan tabbatar da mutuwar wata mata kwatsam sai ga ta da ranta a cikin akwatin gawa a mutuware
Bayan tabbatar da mutuwar wata mata kwatsam sai ga ta da ranta a cikin akwatin gawa a mutuware

Cikin wani rahoto da kamfanin dillanci labarai na AFP ya rawaito, ya bayyana yadda aka dauki gawar mamaciyar a cikin motor asibiti, tare da aiwatar da gwaje-gwaje wadanda a karshe aka tabbatar da mutuwarta. Amma cikin awanni 24 sai ga shi matar ta bayyana a raye.

KU KARANTA: Sojojin sun damke wasu mutane 21 masu hannu a hare-haren da ake kaiwa Filato

A cikin na'urar sanyin da ake ajiye gawawwaki dake wani asibiti a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta kudu.

Wani ma'aikacin dakin ajiye gawarwaki da ke asibitin ne ya fara ankara da faruwar al'amarin, inda ya sanar da likitocin da ke bakin aiki, nan take aka dauke ta zuwa sashin karbar magani.

Wani babban likita ya bayyana matukar al'ajabinsa akan faruwar lamarin, domin sun yi dukkan wani gwajin da zai tabbatar da mutuwar matar, kuma ya tabbatar da ta mutu, amma kuma katsam sai ga shi ta bayyana a raye.

Yanzu dai Wannan mata tana kwance a asibitin domin karbar magani.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng