Na kera rigar bama-bamai sama da 500 ga yan Boko Haram don aiwatar da harin kunar bakin wake – Matashin dan ta’adda
Wani tsohon dan kungiyar Boko Haram mai shekaru 15 wanda aikinsa ne kera bam ya tona asiri kan yadda ya kera rigunan bama-bamai sama da 500 wanda yan ta’adda ke amfani da su wajen aiwatar da kunar bakin wake cikin shekaru biyar da suka gabata.
Ali Goni na da shekara 10 a ajiye shida na makarantar Firamare lokacin aka sace shi a Bama.
Sojoji sun bayyana matashin a matsayin dan Boko Haram mafi hatsari wanda ya san kimiya daban-daban da zai iya halaka rayuka da dama.
Majiyar kwararru na hukumar soji ta sanar da NAN cewa mai laifin ya kasance mafi kwarewa wajen hade-haden bam da aka samu a shekarun bayan nan. Sai dai ba’a bari an dauki hoton shi ba saboda karancin shekarunsa.
KU KARANTA KUMA: Sanata ya bukaci Buhari da yayi murabus kan yawan kashe-kashe da ake yi
Goni, wanda ke fuskantar horaswa a sansanin sojoji dake Maiduguri ya bayyana cewa yana hada bama-bamai daga kananan kayyaki sannan ya harhada su domin kudirin kunar bakin wake.
Ya bayyana cewa ya samar da amfani da dan makuli a jikin rigar bam day an kunar bakin wake za su sanya wanda hakan zai sa na’urar tantance bam baza’a taba bari asan suna dauke da bam ba.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng