Waye zai gaji Sarautar ‘Dan Masanin Kano a Masarautar Kano

Waye zai gaji Sarautar ‘Dan Masanin Kano a Masarautar Kano

- Dukkanin Mai Rai Mamaci Ne, Wannan haka ya ke, domin kuwa mutuwa tana kan mace da namiji, yaro da babba, mai kudi da talaka, mai mulki da wanda ake mulki.

- A rana mai kamar ta yau ne Dr. Yusuf Maitama Sule Dan masanin Kano

A ranar Litinin 3 ga watan Yulin Shekarar 2017 al'ummar kasar nan su ka samu sanarwar rasuwar Alhaji Yusuf Maitama Sule Dan Masanin Kano a kasar Masar, ya rasu ne a kasar ta Masar inda ya yi jinyar rashin lafiyar da ya yi fama da ita.

Waye zai gaji Sarautar ‘Dan Masanin Kano a Masarautar Kano
Waye zai gaji Sarautar ‘Dan Masanin Kano a Masarautar Kano

Marigayi Maitama Sule shaharraren dan siyasa ne a Najeriya, wanda ya rike mukamin minista da kuma jakadan kasar a majalisar dinkin Duniya.

KU KARANTA: Jiki da jini: Sarauniyar Ingila ba lafiya

Sai dai har yau din nan masarautar Kano ba ta nada wanda zai maye gurbin wannan babbar sarauta ta Dan Masanin ba.

Waye zai gaji Sarautar ‘Dan Masanin Kano a Masarautar Kano
Waye zai gaji Sarautar ‘Dan Masanin Kano a Masarautar Kano

Da farko Bayan yan watanni da rasuwar sa aka fara yada jita-jitar za'a maye gurbinsa da tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya, wato Rabiu Musa Kwankwaso.

Sai dai wannan zancen ya zama marar tushe da makama, mutane suna kallon dukkanin wanda za'a nada sarautar Dan Masani to ana Fatan ya Zama mutum mai tarin Ilimin addini da na zamani tare kuma da sanin tarihi.

Amma a wasu masarautun ana nada tsofaffin yan Jaridu sarautar ‘Dan Masani.

Al'ummar jihar Kano da ma na kasa baki daya sun zuba idanu ga masarautar Kanon domin ganin waye zai gaji wannan sarauta ta Dan Masanin Kano.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng