Hirde: Miyetti Allah ta yanke hukuncin daukan mataki kan al’adar badala

Hirde: Miyetti Allah ta yanke hukuncin daukan mataki kan al’adar badala

Shuwagabannin kungiyar Miyetti Allah Kautal-Hori sun bayyana damuwarsu da wata al’adar kabilar Fulani, da ake kira da suna ‘Hirde’, inda suka bayyanata a matsayin mummunar al’ada, don ya zama wajibi a garesu da su tashi haikan don yakar wannan al’ada.

Jaridar Aminiya ta ruwaito shuwagabannin sun dauki wannan mataki ne a yayin wani taro da suka shirya a kauyen Rugan Aso dake cikin karamar hukumar Karu ta jihar Nassarawa, wanda shugaban kungiyar, Abdullahi Bodejo ya jagoranta.

KU KARANTA: Abinda ya kamata kuyi idan har kuna son kama Shekau cikin ruwan sanyi – Kwamandan Boko Haram ga Sojoji

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ita dai wannan al’ada ta Hirde ana gudanar da ita ne a lokuttan bukukuwan Sallah, musamman a tsakanin matasa maza da mata, inda Maza da Mata suke kebewa a dazukka suna saduwa da juna har na tsawon kwanaki, wasu lokuttan har ma da Matan aure.

Da wannan dalili ne Bodejo ya dauki alwashin yin aiki kan jiki kan karfi don ganin kungiyar Miyetti ta kawo karshen wannan mummunan al’ada, da yace tana kulla kiyayya a tsakanin Fulani, don haka yace zasu kafa kwamiti da zai sanya idanu, don kama duk wanda ya karya dokar, musamman a yayin bikin babbar Sallah.

Bodejo ya cigaba da cewa; “Al’adar Hirde na janyo tashin hankali a tsakanin Fulani, musamman idan abin ya hada da Matan aure, haka zalika al’adar ta saba ma koyarwar addinin Musulunci, don haka zamu kawo karshensa, kamar yadda muka yi da Sharo.”

Baya ga batun Hirde, a yayin wannan taro, shuwagabannin kautal-hori sun tattauna matsalolin da suka shafi Fulani, kamar su tallatar nono da Mata masu aure ke yi, karancin ilimin addini da na Boko na yaran Fulani, da batun mallakan katin zabe.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng