Hotuna: Shugaba Buhari a taron gangamin AU a Mauritania
Shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari, na halartan taron gangamin gamayyar shugabannin kasashen Afrika karo na 31 da ake yi yau Lahadi, 1 ga watan Yuli a Nouakchott, babban birnin kasar Mauritania.
Daga cikin jami'an gwamnatin Najeriyan da ke tare da shi a taron sune babban lauyan tarayya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami da ministan harkokin wajen Najeriya, Gepffrey Onyeama.
Legit.ng ta kawo rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari, ya isa birnin birnin Nouakchott, kasar Mauritania da yammacin nan domin halartan taron gamayyar kasashen Afrika wato AU karo na 31 da za’a gudanar ranan 1 da 2 ga watan Yuli, 2018.
Daga cikin wadanda suka jira saukarshi a babban filin jirgin saman Nouakchott sune shugaban kasar Mauritania, Mohammed Ould Abdel Aziz, da wasu manyan jami'an gwamnatin kasar.
Taron na wannan shekaran dai na ke take : “Samun nasara kan yaki da rashawa: Yadda za’a kawo sauyi nahiyar Afrika”. Shugaba Muhammadu Buhari ne zai gabatar da jawabi na musamman akan wannan take.
Sannan shugaban gamayyar kasashen Afrikan kuma shugaban kasan Ruwanda, Paul Kagama, zai gabatar da jawabi kan sauye-sauyen gamayyar, shi kuma shugaban kasan Nijar, Mahamadou Issoufou, zai gabatar da nasa kan kasuwanci a Afirka.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng