Dogara na so a bar wa matasa zalla mukaman karamin Minista

Dogara na so a bar wa matasa zalla mukaman karamin Minista

Kakakin Majalisar wakilai, Hon Yakubu Dogara, ya ba da shawarar a warewa wa matasa zalla mukaman kananan Minista a kasar.

Dogara ya yi wannan kira ne a yayinda ya ke magana a taron bikin murnar amincewa da dokar bai wa matasa damar shiga harkar siyasar kasar.

Ya ce tun farko dama a tarihin gwagwarmayar dimokradiyya, fafutika ce ake yi tsakanin wadanda ake damawa da su da wadanda ba a damawa da su.

Dogara ya ce akasarin wadanda aka maida saniyar-wace a siyasa ko a mulkin kasar nan duk matasa ne.

Dogara na so a bar wa matasa zalla mukaman karamin Minista
Dogara na so a bar wa matasa zalla mukaman karamin Minista

A halin da ake ciki, Dan takarar shugabancin kasa karkashin lemar Peoples Democratic Party (PDP), Dr Datti Baba-Ahmed, ya fada ma jam’iyyar cewa su bashi tikitin takarar shugabancin kasa, cewa zai kora shugaban kasa Muhammadu Buhari gida a zaben shekara mai zuwa.

Ya bayyana hakan ne sakatariyar jam’iyar ta kasa dake Abuja lokacin da ya je kaddamar da kudirinsa na tsayawa takara a ranar Juma’a.

KU KARANTA KUMA: Zan goyi bayan duk wani yunkuri da zai inganta tsaro – Shugaba Buhari ya yi alkawari

Da yake gabatar da kansa a matsayin wanda ya zuba jari wajen cigaban matasa ta hanyar ilimi, dan takarar wanda ya kasance jagoran jami’ar Baze, Abuja ya ce duk da cewar bai samu tikitin ba, zai ci gaba da ba jam’iyyar hadin kai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku bide mu a shafukanmu na kafofin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel