Yanzu Yanzu: Motar tanka ta kama da wuta a babban titin Lagas zuwa Ibadan (hotuna, bidiyo)
Wata babbar motar tanka ta kama da wuta a gadar Otedola dake wajen Lagas.
An tattaro cewa hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Lagas (LASEMA) da hukumar kashe gobara na jihar Lagas na wajen da abun ke afkuwa.
Rundunar yan sandan mai yaki da yan fashi wato SARS ce ta bayyana hakan ta shafinta na Twitter @rrslagos767.
Hukumar RRS tace jami’anta na kasa domin magance lamarin.
A cewar shaidu da abun ya afku a idanunsu, sunce wutan ya lashe sama da motoci 20 da kuma wasu mutane da ba’a san adadinsu ba akan gadar ta Otedola, babban titin Lagas zuwa Ibadan.
KU KARANTA KUMA: Jakadan Najeriya a Saudiyya ya musanta zargin daukar ma’aikata a boye
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng