Baza mu sake zuwa aikin hajji ba - Limaman kasar Tunusiya

Baza mu sake zuwa aikin hajji ba - Limaman kasar Tunusiya

Manyan limaman kasar Tunusiya sunyi kira ga Muftin kasarsu daya yi kokarin ‘yantar da jama’arsu daga aikin hajji, ganin yanda farashin kujerun zuwa kasar Saudiyyan ke ta faman karuwa, sannan kuma sunyi ikirarin cewa kasar ta Saudiyya tana amfani da kudin musulmai masu zuwa aikin hajji wurin yakar al’ummar musulman duniya

Baza mu sake zuwa aikin hajji ba - Limaman kasar Tunusiya
Baza mu sake zuwa aikin hajji ba - Limaman kasar Tunusiya

Manyan limaman kasar Tunusiya sunyi kira ga Muftin kasarsu daya yi kokarin ‘yantar da jama’arsu daga aikin hajji, ganin yanda farashin kujerun zuwa kasar Saudiyyan ke ta faman karuwa, sannan kuma sunyi ikirarin cewa kasar ta Saudiyya tana amfani da kudin musulmai masu zuwa aikin hajji wurin yakar al’ummar musulman duniya.

DUBA WANNAN: Tsohon Kocin kasar Masar ya mutu, saboda cin su da kasar Saudiyya tayi

Gidan rediyon Shems dake kasar Tunusiya sune suka rawaito wannan labari, inda suka ce sakatare janar na kungiyar manyan limaman kasar, El Fadel Ashur ya kira Muftin kasar ta Tunusiya da murya mai karfi akan ya fitar da fatawar da zata saka musulman kasar su daina zuwa aikin hajji.

A yanda limaman suka fada a shafin watsa labarai na ‘Algerie Focus’, sun bayyana cewar a ‘yan shekarun nan farashin kujerun aikin hajji sunyi tsada sosai, sannan kuma irin dumbin kudaden da kasar Saudiyya take tarawa, tana amfani dasu ne wuin yakar al’ummar musulman duniya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng