Kiristoci masu zanga-zanga sun tafka barna a gidan gwamnatin Plateau

Kiristoci masu zanga-zanga sun tafka barna a gidan gwamnatin Plateau

- Sakamakon rikicin da ya barke a jihar Plateau, mabiya addinin Kirista a jihar sun fara zanga-zanga

- Sai dai zanga-zangar ta rikide ta haddasa barnar dukiyar gidan gwamnati

- Har sai da ta kai 'yan sanda sunyi barazana kafin tarwatsa masu zanga-zangar

Cincirundun mata da matasa da suka taro don nuna rashin amincewarsu da irin hare-haren da ake kaiwa sassan jihar musamman a karamar hukumar Barkin Ladi da yayi sanadiyyar rasa rayuka da dama.

Kiristoci masu zanga-zanga sun tafka barna a gidan gwamnatin Plateau
Kiristoci masu zanga-zanga sun tafka barna a gidan gwamnatin Plateau

Sai dai kuma masu gudanar da zanga-zanga sun yi barna mai yawan gaske a gidan gwamnatin jihar Plateau, inda suka faffasa kofofin gilasai da kuma gilasan motocin da aka ajiye a farfajiyar gidan gwamnatin.

Amma kuma kafin wannan zanga-zanga ta yau an jiyo shugabannin kungiyar mabiya addini Kirista na Arewacin jihar yana bayar da umarni ga duk mambobin kungiyar da su zauna a gida yau da kuma gobe kafin su fara zanga-zangar a fili.

Masu gudanar da zanga-zangar sun harzuka ne biyo bayan rashin samun gwamnan a gida a lokacin kasancewar ya tafi raka shugaban majalisar dattijai Sanata Abubakar Bukola Saraki bayan ya kammala ziyarsa ta taya gwamnan jimami abinda yak faruwa zuwa filin jirgin sama.

Duk wani yunkuri da darakta yada labaran gwamnan jihar Emmanuel Nanie yayi na kwantar da hankulan masu zanga-zangar ya ci tura, har sai da ta kai jami'an tsaro sunyi harbi sama kafin su iya tarwatsa su.

KU KARANTA: Adadin mutanen da suka mutu a harin da aka kai kauyukan Plateau ya tasar ma 100 – Yan sanda

A da dai CAN din ta bayar da sanarwa kamar haka; “CAN ta Arewacin jihar Plateau ta bayar da umarnin kowanne mambanta da ya zauna a gida a yau da gobe ba tare da shiga wata mu’amala ta aiki, sana’a ko fita kasuwa ba don nuna alhinin yawaitar kashe-kashen da yake faruwa.

Sannan kowa ya fito a gobe domin gudanar da gagarumar zanga-zanga da iyayenmu mata da matasa zasu jagoranta a gobe Alhamis a shataletalen tsohon titin jirgin saman jihar da misali karfe tara 9:00am na safe".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel