Ragowar manyan jiragen ruwan nan 8 sun iso Najeriya makare da kaya
- Da alamun farashin kaya zai kara sauka a Najeriya
- Karin wasu jiragen ne cike da kayan amfani suka iso Najeria
Rahotan da yake iske mu wanda kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito, ya nuna cewa yanzu haka maganar da ake ragowar karin wasu manyan jiragen ruwa takwas sun iso Najeriya makare da kaya.
Hukumar kula da shige da ficen kaya ta gabar ruwan Najeriya (NPA) ce ta tabbatarwa da NAN cewa, jiragen dai sun iso gabar tekun Najeriya dake jihar Legas a yau Talata makare da kaya.
KU KARANTA: Da dumin sa: Shugaba Buhari ya bude wani katafaren asibiti da rukunin gidaje 100 na sojin sama a Calabar
NPA ta bayyana cewa 4 daga cikin sundukin dakon kayan ya kunshi man fetir yayin da karin wasu 4 ke makare da man dizal da na man jirgi da kuma taki.
Sannan ta kuma shaida cewa 30 daga cikin sundukan dakon kayan sun kunshi kayayyaki madanganta man fetir (man hada man shafawa bakin mai da sinadarin hada kwalta) da kayan abinci da sauran kayayyaki.
Sannan kuma hukumar na tsammanin sake samun karin isowar wasu jiragen ranar 26 zuwa 30 ga watan nan da muke ciki (Yuni) da suka dauko dakon kayan alkama, taki, fetir da sauransu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng