Hukumar NDLEA ta damke dilolin kwaya 443 a jihar Katsina

Hukumar NDLEA ta damke dilolin kwaya 443 a jihar Katsina

Hukumar hana fasa kwabrin muggan kwayoyi wato NDLEA a yau Talata ta alanta damke masu safarar muggan kwayoyi 443 rike da akalla kilo 336.4043 na kwayoyi da lita codeine 2,553.06 cikin wattani shida.

Hukumar ta kara da cewa ta gurfanar da guda 23 cikinsu kuma akwai sauran 110 da ake shari’arsu a yanzu a babban kotun tarayya da ke jihar Katsina.

Kwamandan NDLEA na jihar, Maryam Gambo Sani, wacce ta bayyana hakan a wani hira da manema labarai ta ce an damke kwalaben Codeine 24,000, kilon cannabis sativa 51, kilon Tramol 53 a Funtua, Sandamu, da Katsina.

KU KARANTA: Daga karshe Rahma Indimi ta yi magana akan baikon kanwarta

Ta kara da cewa hukumar ta damke daliban makaranta 21 da kananan yara yan kasa da shekaru 13 a kwalaben Codeine 128.

Yayinda yake kukan yawaitan ta’amuni da muggan kwayoyi a jihar Katsina, ta yi kira ka iyaye, shugabanni makarantu da su ja kunnen yara kan illolin muggan kwayoyi.

Ta jaddada niyyar hukumar ta tabbatar da cewa an cimma manufar kawo karshen ta’amuni da muggan kwayoyi game da shirin National Drug Control Master Plan (NDCMP) a jihohi da kananan hukumomi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel