Daga karshe Rahma Indimi ta yi magana akan baikon kanwarta
Al’amarin bikin Muhammed da Hauwa na kara gabatowa, masoyan da lamarin aurensu ya janyo cece-kuce za su hau turban girma a watan Yuli.
A baya Legit.ng ta rahoto wani labari da yayi ikirarin cewa Muhammad tsohon saurayin ýaýar Hauwa ne wato Fatima.
Haka zalika ya taba soyayya da Zahra Buhari wacce ta kasance suruka ga Indimi.
Tun da aka yi baikon su, babu ko daya daga cikin yan uwan Hauwa da ta wallafa labarin a shafin zumunta don taya yar’uwar ta su murna.
Rahma Indimi ta karya shirun ta, domin ta je shafinta na Instagram don taya kanwar tata murna tare da bata shawarar cewa ta zamo mata ta gari ga mijinta.
KU KARANTA KUMA: Ina farin ciki na hana kaina da ma’aikatana amfana da kwangila - Buhari
Ta bayyana yadda ta shiga kokwanto lokacin da ta hotunan kafin auransu, ko ta wallafa ko kuma ta bari auran ya kusanto.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng