Hanyoyi 5 da zaku bi don ɗaukar hankalin abokin zamantakewa

Hanyoyi 5 da zaku bi don ɗaukar hankalin abokin zamantakewa

- A zamantakewa irin ta yau da kullum akwai abubuwa da dama wanda ya kamata masoya ko ma'aurata ya kasance suke yi domin zai taimaka gaya wajen kara musu karsashi da dankon soyayya da kuma san kasancewa da juna a ko da yaushe

Wannan ba komai bane face kula da kai ta yadda za’a kasance wajen inganta surar jiki wanda hakan ne zai sa kaji abokan zama suna kaunar kasancewa ba tare da kosawa da junansu ba. Ga kadan daga cikin wadannan hanyoyi:

Hanyoyi 5 da zaku don ɗaukar hankalin abokin zamantakewa
Hanyoyi 5 da zaku don ɗaukar hankalin abokin zamantakewa

1 Tabbatar da surar jiki mai kyau ta hanyar motsa jiki

Wannan hanya ce mai kyau kamar yadda likitoci suke bayani tare da nuna fa'idar Motsa jiki ga dan Adam, tabbas wata hanya ce da zata sa gangar jiki ta zama tana cikin koshin lafiya kuma zata taimakawa mutum ya kasance cikin ƙirar jiki mai kyau kuma gwanin ban sha'awa wanda kowa zai yi burin sake kallon surar jikinka musamman abokin zamantakewar

2 Gyaran Gashi ko Suma

Ba ga mata kawai ba hatta ma maza wannan yana daya daga cikin hanyoyi masu amfani wajen gyaran jiki. Idan mace ce yana da kyau lokaci zuwa lokaci take gyaran gashin ta sannan take kula da shi yadda ya kamata, domin hakan zai kara mata kwarjini. Har wa yau yana kara kyau ga mace take yin nau'in kitso daban-daban masu daukar hankali wanda zasu kara mata kyau musamman ga mai gidanta.

Idan aka dawo bangaren maza, yana da kyau a ce mutum yana da wani lokaci da ya warewa wanda zai ke aske gashin kansa ko da kuwa ba duka ba kamar dai yadda wasu ke yi. Hakan ya hada da gyara ƙasumba da duk sauran wani nau'in gashi na zahiri dana boye.

KU KARANTA: Jerin ƙaryayyaki 5 da samari ke zulawa ƴan mata a yayin da suke tsaka da soyayya

3 Kwaliyya

Mata iyayen giji sannan an ce wajen ado aka san su. Tabbas abu ne mai kyau ga 'ya mace ta kasance mai yin kwalliya domin tana da muhimmancin gaske a zamantakewa ta yau da kullum. Domin tana hana maza kallon wasu matan na daban a waje musamman idan macen ta kasance gwanar iya ado ce.

4 Shan wadataccen Ruwa

Ruwa ya kasance wani irin sinadari ne mai matukar amfani a jiki, kuma shan sa sosai yana hana garkuwar jiki kamuwa da wasu cututtuka. Baya ga wannan shan ruwa yana taimakawa fatar jikin mutum ta kasance cikin koshin lafiya ta hanyar hana yin kuraje, makero da sauran cututtuka na fata. Idan kuwa aka ce fata ta kasance mai lafiya to tabbas zaka same ta mai daukar ido da hankalin mai kallo.

5 Amfani da Turare da Mayuka masu sa ƙamshi

Tsafta dai kamar yadda aka sani cikon addini ce, yana da kyau ba wai dan wani ya gani ba ko dan karan-kanka ya kamata a ce mutum yana yiwa kansa tsafta.

Amfani da mayuka ko turare na sa kamshin jiki abu ne mai muhimmancin gaske domin duk inda ka shiga zaka kasance cikin kamshi mai dadi sannan kowa zai ke muradin zama kusa da kai, amma idan aka ce an samu sabanin haka tabbas kowa zai guje ka.

Akwai Turare da mayuka daban-daban na gyaran jiki wanda in har ana amfani da su tabba dole abokanan zamantakewa suke sha'awa tare da kaunar kadancewa da juna.

Kamar yadda ciki yake bukatar a ba shi abinci lokaci zuwa lokaci, haka ya zama dole ga mutum yake kula da kansa kama daga abinci, kula da fatar jiki, sutura da dai sauransu ya zama dole saboda rashin yin hakan zai iya zama tawaya ga masoya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel