Kofin Duniya: Fasha aka yiwa Najeriya inji Drogba
- Da walakin goro a miya inji masu iya magana
- Wasan karshe na cikin rukinin da Najeriya da buga jiya da kasar Argentina ya bar baya da kura
- Inda tsohon dan wasa chealsea Drogba yake ganin busar an yi fasha
Tsohon dan wasa gaba na kungiyar Kwallon kafa ta Chelsea da kuma kasar Ivory Coast, Didier Drogba ya ce rashin alkalanci mai kyau shi ne ya bawa kasar Argentina damar doke kasar Nigeria a gasar cin kofin duniya a jiya talata.
Toshon dan wasan ya bayyana hakan ne a yayin da yake tattaunawa da BBC, inda ya bayyana cewa alkalin wasan ya yiwa kasar Argentina adalci wajen hana bugun daga-kai sai mai tsaron raga, wanda Nigeria ta samu a dalilin taba kwallon da ɗan bayan kasar Argentina ya yi da hannusa.
Dan wasan yace "Alkalin bai yi adalci ba saboda da ya duba da kyau zai gano cewar an taɓa kwallon da hannu wanda hakan kuskure ne, amma abu ne mai wuya ya bada bugun daga-kai sai mai tsaron raga saboda Argentina zata iya ficewa daga gasar in har hakan ta faru".
Kasar Argentina dai ita ce ta fara saka ƙwallo a raga ta hannun dan wasanta Lionel Messi a kashin farko na wasa, wanda daga bisani Nigeria ta farke ta hannun dan wasan gefe Victor Moses daga bugun daga kai sai mai tsaron raga a minti na 51.
KU KARANTA: Da yiwuwar Argentina zata kori Messi idan basu ci Najeriya yau ba
Nigeria ta samu damarmamaki wanda ya kamata ace tayi amfani da su, amma hakan bai yiwu ba, ta kuma sake samun wata dama ta hannun dan wasan gabanta Ighalo wanda ya kamata ace ya saka kwallon a raga amma sai ta taba hannun dan wasan baya na kasar Argentina.
Alkalin wasan ya hana bugun daga kai sai mai tsaron raga bayan da yaje ya duba na'urar bayan fili domin tattabar da abinda ya faru.
Argentina ta sake zura kwallo a ragar Nigeria ne ta hannun dan wasan bayanta Marcos Rojo a minti na 86 lokacin da wasan yake dab da karewa.
Yanzu haka dai Nigeria ta biyo sahun sauran kasashen Afrika da suka fice daga gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar Russia kamar su Egypt, Tunisia da kasar Morocco.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng