Rikicin makiyaya da manoma: Buhari yana bakin ciki kan yadda ba’a mutunta ran dan Adam a Najeriya

Rikicin makiyaya da manoma: Buhari yana bakin ciki kan yadda ba’a mutunta ran dan Adam a Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari bayyana bacin ransa da kashe kashen dake faruwa a Najeriya, inda yace ran dan adama bai zama a bakin komai ba a Najeriya, ya zama banza, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Buhari ya bayyana haka ne a ranar Litinin, 25 ga watan Yuli akan hare haren da aka kai jihar Filato, inda aka yi asarar rayuka sama Tamanin, inda ya danganta lamarin ga wasu mutane dake yin duk mai yiwuwa don ganin sun tayar da hankula don su samu biyan bukata a zabe mai zuwa.

KU KARANTA: Matar wani gwamnan Arewa ta biya ma wata mara lafiya naira N1,300,000 kudin asibiti

Buhari ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawusa, Garba Shehu, inda yace gwamnatinsa na sane da yunkurin da yan siyasa ke yi don ribatan rikice rikicen nan; “Mun san akwai bukatu iri iri daku rura rikice rikicen nan, haka zalika muna sane da yunkurin yan siyasa.

Buhari yana bakin ciki kan yadda ba’a mutunta ran dan Adam a Najeriya
Buhari

“Labarin da muka samu shine wasu kabilu sun sace ma Fulani sama da shanu dari, tare da kashe wasu daga cikin Fulanin, bayan nan sai gwamnan jihar Filato ya kira makiyayan da abin ya shafa, inda ya basu hakuri, kuma ya basu tabbacin zai nema musu hakkinsu, amma kwatsam cikin kasa da awanni 24 sai rikici ya barke.

“Hakan na faruwa sai wasu yan daba suka shiga fasa shagunan mutane, tare kai ma abokan hamayya a siyasance hari, har ta kai ga suna tare motoci suna kashe mutane idan ka nuna baka tare da wata jam’iyya” Inji Buhari.

Sanarwar ta cigaba da cewa hatta gwamnan jihar, Simon Lalong da kansa ya fatattaki wasu daga cikin yan daban nan da suka sanya shingen kan hanya suna tare mutane, a hanyarsa ta komawa gida daga babban birnin tarayya Abuja.

Daga karshe Buhari yayi kira ga duk wadanda rikicin manoma da makiyaya ya shafa da lallai su kyale doka tayi aikinta, kada su dinga daukar doka a hannunsu, sa’annan yace sun aika jami’an tsaro jihar don kare sake barkewar rikicin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng