Sirrin kiyaye hada hanya da hawan jini daga bakin masana
- Da magani a gonar yaro amma bai sani ba inji masu iya magana
- Hawan jini na daya daga cikin cutar da ta zama ruwan dare musamman ga mutanen da girma ya zo musu
- Sai dai yau wani likita ya farkewa cutarr laya
Wani kwararran likita mai suna Dr Abdul-Afeez Adeniji ya shawarci ‘yan Najeriya da su rage aikata abubuwa guda uku da ka iya jefa rayuwarsu cikin hadarin kamuwa da ciwon hawan jini.
Likitan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) hakanne yayin gangamin gwajin hawan jini da gidauniyar Sabitu Adeniji ta shirya a jihar Legas ranar Lahadin da ta gabata wanda a kalla mutane 65 ne aka tantance, a watan Afrilun da ya wuce an ma dai an tantance muatne 100 a tsarin farko na shirin.
A cewarsa daga cikin manyan abubuwan da suke haddasa ‘yan Najeriya suke yawan kamuwa da cutar ta hawan jini akwai;
1 - Shan gishiri mai yawa
Rage shan gishiri kan taimaka wajen rage yiwuwar kamuwa da hawan jini kuma kan kara karfin kashi musamman ga manya mutane da shekarunsu suka ja.
2 - Shan Sigari
Ba wai lallai sai sigari ba, duk wani nau’i na kayan hayaki da ake shaye-shaye da shi a shaka a busa ya kan sanya mai wannan harka cikin sahun gaba na hadarin kamuwa da ciwon hawan jini.
KU KARANTA: Kalar abubuwa 7 da suke bawa Hanta matsala, na 7 mutane da yawa na sha
3 - Shan Giya
Dama dai sun ba yau ba Legit.ng ta sha kawo muku rahotanni iri-iri kan yadda shak giya kan hadda cututtuka daban-daban, yau ma ga shi kwararren masani ya sanyo ta cikin abubuwan masu kaya masu hadarin gaske da ka iya jefa mai ta’ammali da ita kamuwa da hawan jini wanda yake ya zama tamkar ruwan dare a yanzu.
Daga karshe Dr Abdul-Afeez Adeniji ya ja hankalin mutane da karda su dauka cewa yawaitar ciwon kai alamar ciwon zazzabin cizon sauro ne kawai, a’a a cewarsa zai iya zamowa alamar ciwon hawan jini ne.
A saboda haka ne ya shawarci mutane da su rika ziyarta likita akai-akai domin duba lafiyarsu da sunji bakon abu a tare da su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng