Bayan korar Farfesa mai neman mata, jami'ar ta gano ashe yarinyar ma taci kwas din ya maqale ta
- An kori Farfesan bayan da aka gano lallai ya aikata tsiyar
- An kuma gano ashe ta ma ci kwas din amma ya qi gaya mata
- An ganoo karin karairayin da yayi mata
Jami'ar OAU ta saki bayanan karshe kan batun da ya zaga duniya na wata yarinya da malaminta ke neman ta kwanta dashi domin ta haye kwas dinsa. Monica Osagie dai, ta tona asirin ne, bayan da Dattijon ya fito baro-baro ya nuna sai ya kwanta da ita sannan zata haye zuwa karatu na gaba.
Ita kuwa ta kwape hirarsu dashi, inda ta tuttura wa jama'a har duniya ta dauka, wanda hakan ya janyo aka kafa kwamiti tare da dakatar da bunsurun daga koyar da 'yan mata.
Karshe dai, bayan borin kunya ya boye shi, ya fito ya fuskanci kwamtin da makaranta ta kafa, inda daga karshe, aka kore shi daga aiki a jami'ar.
DUBA WANNAN: Hukuncin kisa ga shaihun Malami a wata kasa
Bayan nan kuma, an gano ashe ma taci kwas din nasa, kawai kisisina ce ta sa yace mata bata ci ba, don kawai ya samu ya biya bukatarsa.
Ya dai amsa laifukansa, na kwanciya da mata da yawa, ya kuma nemi tuba, ya kuwa tattara komatsansa ya bar gidan gwamnati, kamar dai tasa ta qare.
Ko'ina dai ana samun irin wannan danyen aiki, kawai tasa ce ta fito fili, malamai sai ayi hattara.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng