Buhari a Bauchi: Mai daga hoton Buhari dan wahala ne - Inji wasu 'yan Najeriya
Ko dai bai zo na daya ba, shugaba Muhammadu Buhari na daya daga cikin 'yan Najeriya da suka fi kowa farin jini a tarihin kasar tun bayan shigar sa siyasa a shekarar 2002.
Shi dai shugaba Buhari din yana da dumbin magoya baya na ban mamaki musamman ma jihohin arewacin kasar nan inda wasu kan shafe tsawon kilomitoci a kafa suna tafiya tare da kashe kudaden su duk domin su yi ido biyu da shugaban a duk inda ya je.
KU KARANTA: Rigima kwance saboda cushen da majalisa ta yi a kasafin kudi
Legit.ng ta samu cewa a ranar Alhamis din da ta gabata ne dai shugaban kasar ya ziyarci jihar Bauchi domin jajantawa 'yan jihar da ibtila'in ruwa hade da iska ya yiwa barna.
Wajen taron masu tarbar sa ne dai aka ga wani tsoho dauke da hoton shugaban kasar a kafadar sa wanda hoton yayi farin jini sosai musamman ma a kafafen sadarwar zamani inda mutane da dama suka bayyana ra'ayin su game da shi:
Ga dai wasu daga cikin ra'ayoyan kamar yadda BBC Hausa ta wallafa:
Haka zalika Gazali Muhammad Adc Shuniya ce: "Son masoyin wani koshin wahala. Talakawa na soun Shugaba Buhari yayin da shi kuma baya sun su."
Saminu T Usmancewa ya yi: "Dan wahala ne. Maimakon ya riko hoton aikin da yake so a yi masa a jiharsa, amma ya bige da wannan."
Mariya M Aliyucewa ta yi:
"Hakika jihar Bauchi ta cancanci Baba yaje mata, koda kuwa wasane yakaishi, ba jajeba, duba da yadda duk Najeriya,ba jihar da ta kunshi'yan gani kashenin Babairin Bauchi."
Shi kuma Usman Abdu raddi ya yi wa magoyin bayan Buharin:
"Wannanya hadu da wahala.Ya tafi kawai yaso annabi (SAW). Gashi yunwa tayi masa illa."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng