Cin kofin duniya: Abubuwa 5 da suka sa Najeriya ta doke kasar Iceland

Cin kofin duniya: Abubuwa 5 da suka sa Najeriya ta doke kasar Iceland

Tun bayan kyakkyawar kwallon da 'yan kasar Najeriya suka buga a wasan su na jiya da ya farantawa 'yan kasar da dama rai, masana harkokin wasannin sun dukufa wajen yin fashin baki.

Masana da dama dai na ganin daman wasan farko da kasar ta buga da kasar Kuroshiya mai horar da tawagar 'yan kasar ya tafka kura-kurai da dama ne wanda yayi sanadiyyar rashin katabus daga 'yan wasan.

Cin kofin duniya: Abubuwa 5 da suka sa Najeriya ta doke kasar Iceland
Cin kofin duniya: Abubuwa 5 da suka sa Najeriya ta doke kasar Iceland

KU KARANTA: An fiddo Ahmed Musa takarar shugaban kasa a 2019

Legit.ng yanzu haka dai ta tattaro maku wasu daga cikin sauye-sauyen da ka iya zama sandaiyyar kokarin 'yan wasan kasar a wasan da suka buga da kasar Iceland suka kuma doke su da ci 2 da nema.

1. Sauya salon wasa: A maimakon buga 'yan wasa 4 da yayi a wasan Najeriya da Kuroshiya, a wasan jiya an sanya 'yan wasa 3 ne kuma dukkan su masu tsawo.

2. Sauyawa wasu 'yan wasan wuri: Mai horar da 'yan wasan ya sauyawa wasu fitattun 'yan wasan wuri musamman ma dai Mikel Obi, Ahmad Musa da kuma Moses.

3. Farawa da Ahmad Musa: A maimakon farawa da Iwobi kamar wasan farko, kocin Najeriya ya fara da Ahmad Musa wanda kuma yayi kwazo sosai.

4. Yanayin zafi: Yanayin zafin wurin da akan buga wasan ya taimaki 'yan wasan Najeriya sosai.

5. Taka tsan-tsan: Duk da dai an bugawa Najeriya bugun daga-kai-sai-mai-tsaron gida, amma dai a iya cewa 'yan wasan sun yi wasa mai tsafta ba su samu jan kati ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng