Hotunan motar alfarma ta Naira miliyan 108 da wani fitaccen malamin addini ya siya

Hotunan motar alfarma ta Naira miliyan 108 da wani fitaccen malamin addini ya siya

- Yanzu haka dai labari ya zagaye gari cewa fitaccen malamin addini a kasar Ghana ya sayi motar kece raini

- An ce dai Faston mai suna Daniel Obinim ya sayi motar ne kan kudi Naira miliyan 108

- Haka ma an ce yanzu Faston yana da motocin alfarma da dama ciki hadda masu sulki

Labarin da muka samu na nuni ne da cewa jagoran rukunin majami'un nan na International Godsway a kasar Ghana mai suna Fasto Bishop Obinim yanzu haka ya sayi wata babbar motar alfarma kirar Ghost Series II.

Hotunan motar alfarma ta Naira miliyan 108 da wani fitaccen malamin addini ya siya
Hotunan motar alfarma ta Naira miliyan 108 da wani fitaccen malamin addini ya siya

KU KARANTA: Kiristocin Arewa sun yi kaca-kaca da hadimar Buhari

A baya dai babban Faston daman ya taba bugun gaba cewa yana da motoci kirar Rolls Roys har guda takwas amma dai da alama wannan sabuwar duk ta dara su kyau da tsada.

Legit.ng ta samu cewa Faston dai daman yana daya daga cikin malaman addinin kiristan dake rayuwar jin dadi a Nahiyar Afrika kuma ko a makon da ya gabata ma ya je yawon shakatawa da matar sa a kasar Sifen.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng