Dokin zuciya: Neman budurwa daya ya sanya wani mutum cinnawa dayan wuta

Dokin zuciya: Neman budurwa daya ya sanya wani mutum cinnawa dayan wuta

- Kishi kumallon mata, amma a yau kishin ya zama kumallon maza

- A jihar Naija wani mutum ne yayi balangun abokin takararsa

- Tuni jami'an 'yan sanda suka damko shi kuma har suna shirin gurfanar da shi gaban kotu

Neman aure cikin nema ya sanya wani mutum da aka bayyana sunansa da Baba Muhammed mai shekaru 45 cinnnawa abokin karawarsa Usman Tetengi wuta a jihar Naija.

Yanzu haka dai bayan babbaka abokin neman budurwar tasa Mohammed dan asalin kauyen Baba Edo ne dake karamar hukumar Lavun a jihar na can a hannun jami’an ‘yan sanda.

Neman budurwa daya ya sanya wani mutum cinnawa dayan wuta
Neman budurwa daya ya sanya wani mutum cinnawa dayan wuta

Tun da farko a cewar Muhammed ya gargadi Usman da hawainiyarsa ta kiyayi ramar matar da zai aura don kuwa har yayi tambaya amma Usman din yaki ji balle ya saurara.

Sannan ya bayyanawa ‘yan sanda cewa ya dauki matakin ne domin yayi duk mai yiwuwa don ganin usman din ya kyale masa matar da yake mutukar son aura, kuma ko kusa ba ya nadamar wannan aika-aika da yayi.

KU KARANTA: Yanzu – yanzu: Sama ko kasa, an nemi alkalin da zai shari’ar El-Zakzaky an rasa

“Ba na nadamar abinda na aikata saboda inda ban kashe shi a lokacin ba da ni zai kashe, gara ya tafi can don kar ma ya sake hada hanya da ni”

“Ban yi aure ba, kuma ban damu da duk matakin da zai biyo baya ba, abu mai muhimmanci kawai shi ne nayi maganinsa daga shiga sabga ta. Akwai mata da yawa amma sai ya zabi ya cigaba da neman matar da na riga da nayi tambayar aurenta, hukuncin da na dauka shi ne ya dace da shi”. Baba ya jaddada.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Muhammad Abubakar ya bayyana cewa wanda ake zargin ya aika wani yaro ne mai suna Abdul ya siyo masa kwalba uku na fetir wanda yayi amfani da shi wajen babbaka abokin neman budurwar tasa.

Abubakar ya ce anyi sauri an garzaya da wanda iftila’in ya faru da shi cibiyar kula da lafiya ta tarayya (FMC) dake Bida daga basani kuma aka mayar da shi zuwa asibitin Gwagwalada na Abuja inda ya cigaba da karbar magani kafin daga bisani rai yayi halinsa.

Kuma za’a kai maganar gaban alkali da zarar an kammala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng