An damke jami’an yan sandan bogi masu yiwa mutane fashi
An damke wasu masu garkuwa da mutane da kuma fashi da makami masu amfani da mota kalan yan sanda da kuma kayan yan sanda a jihar Ribas.
Jami’an yan sandan SARS sun damkesu ne a ranan Litinin 18 da Talata 19 ga watan Yuni, 2018 inda suka kwato bindigogi da kayan yan sanda a hannunsu.
Yan bindigan sun kasance suna amfani da kakin yan sanda wajen tare mutane a kan hanya. Sunayensu sune Tony Raphael, Ifeanyi Okoye, Chigozie Onuigbo, Emeka Nwaiwu, Clark Sunday da Chinedu Isia.
Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa Jami'an hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Ogun sun tabbatar da damke wasu 'yan fashi guda biyu a garin Kara dake daf wata gada a kan babbar hanyar Lagos zuwa Ibadan yayin da suke shirin fara tare hanyar domin fashi ga masu ababen hawa.
Kakakin hukumar 'yan sanda a jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya sanyawa hannu kuma ya mika ta ga jaridar Tribune Metro.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng