Dubun shugaban ‘yan sara suka da wasu tsageru 32 ta cika, ‘yan sanda sunyi ram da su

Dubun shugaban ‘yan sara suka da wasu tsageru 32 ta cika, ‘yan sanda sunyi ram da su

- Ruwa ya karewa dan kada, shugaban 'yan sarasuka da 'yan barandarsa sun fada komar 'yan sanda

- An gurfanar da su a gaban kuliya har ma alkali ya tura keyarsu kurkuku

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Plateau ta sanar da nasarar cafke shugaban ‘yan hatsabibiyar kungiyar tsageru nan ta ‘yan sarasuka tare da karin wasu mambobin kungiyar 32.

Dubun shugaban ‘yan sara suka da wasu tsageru 32 ta cika, ‘yan sanda sunyi ram da su
Dubun shugaban ‘yan sara suka da wasu tsageru 32 ta cika, ‘yan sanda sunyi ram da su

A ranar Litinin da ta gabata ne dai ‘yan kungiyar sarasukan suka tafka mummunar barna a yankin Bulbula cikin wata unguwa mai suna Congo Russia, inda suka kashe mutane biyu tare da barnata dukiya mai tarin yawa.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar ASP Terna Tyopev ya shaida cewa, “Biyo bayan wannan ta’asa ne ya sanya rundunar ‘yan sandan ta zurfafa bincike har ta samu nasarar damke shugaban kungiyar Umar Ibrahim alias wanda yayi kaurin suna da “Dangari”.

KU KARANTA: Kowa ya hau motar kwaɗayi: Kotu ta yankewa wasu ƴan uwa biyu hukuncin wata 6 a dadlin satar TV plasma

Yanzu haka dai bayan tatsar muhimman bayanai daga wurin shugaban kungiyar tare da mambobinsa, ‘yan sandan sun gurfanar da su gaban kuliya a jiya 20 ga watan Yuni bisa zarginsu da laifukan da suka hada da; hadin kai wajen cutar da al’umma da ta’annati da kuma mallakar muggan makamai masu hadarin gaske.

Jawabin kakakin ‘yan sandan ya nuna cewa yanzu haka har alkali ya ingiza keyarsu zuwa gidan yari sannan da ya dage shari’ar zuwa ranar 25 ga watan Yuni 2018.

Kana kuma sun kama wani kunshi guda 95 na tabar wiwi da kwayar Tramadol ninki 23 da wasu manyan wukake da layu da guraye duka mallakar wadanda ake zargin.

Saboda hakan ne rundunar ‘yan sandan ta bukaci jama’ar gari da su tabbata sun kai duk wasu bayanai da zasu taimaka mata don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel