Jerin sunayen mutane 28 da Buhari ya nadasu mukamai a fannin Shari’a
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin mukamai na mutane 28 a fannin shari’a, da zasu yi aiki a Kotun daukaka kara, babbar kotun tarayya, da kuma babbar kotun birnin tarayya Abuja, inji rahoton jaridar The Nation.
Daga cikn sabbin nade naden, guda goma sha biyu na Kotun daukaka kara, guda Tara na manyan Kotunan tarayya, sai kuma guda bakwai na babbar kotun birnin tarayya, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
KU KARANTA: Rai bakon Duniya: An tsinci gawar yara 5 tare da na mahaifiyarsu, Ubansu ya tsallake rijiya da baya
Kaakakin hukumar shari’a ta kasa, NJC, Soji Oye ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Laraba, 20 ga watan Yuni, inda yace Buhari ya amince da daga likafar Mai sharia Gabriel Kolawole, Bilkisu Aliyu, Abubakar Mahmud Talba da Mohammed Idris zuwa Kotun daukaka kara.
Haka zalika, Mai sharia Folashade Ojo, P.A Mahmud, I.A Andenyangsto, Ebiowei Tobi, J.G Abundaga, A.S Umar, A.M Bayero da A.M Lamido suma duk an tura su zuwa Kotun daukaka kara.
Daga cikin wadanda aka kara musu girma zuwa babban kotun tarayya sun hada da mai sharia Peter O. Lifu, Sunday Bassey Onu, Adefunmilola Adekemi Demi-Ajayi, Obiora Atuegwu Egwuata, Sa’adatu Ibrahim Mark, Mobolaji Olubukola Olajuwon, Aminu Bappa Aliyu, Tijjani Garba Ringim da Nkeonye Evelyn Maha.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng