Rushewar kofar Mata na haifar da dimuwa a Kano

Rushewar kofar Mata na haifar da dimuwa a Kano

A cikin watan da ya gabata, muka samu labarin faduwar ginin nan mai kunshe da tsohon tarihi wato Kofar Mata, bayan wata babban mota ta rufta kan ta, lamarin da ya sa a yanzu sai kufenta.

A shekarun 1400 ne, Sarkin Kano Muhammadu Rumfa, ya gina wannan kofa lokacin da ya bunkasa garin Kano amma an sake gina kofar a shekarar 1985, kafin rushewarta na baya-bayan nan.

Mutanen Kano na cigaba da bayyana alhininsu a kan rushewar wannan kofa, mai tsohon tarihi.

Mafi akasarin dake zaune a garin Kano sun nuna rashin jin dadin faduwar kofar, musamman ganin tasirin da take da shi ga al'adun al'umma, kamar a lokacin hawan sallah, inda sarki kan fita da kuma dawowa ta kofar sa'ilin gudanar da hawan Nassarawa.

Rushewar kofar Mata na haifar da dimuwa a Kano
Rushewar kofar Mata na haifar da dimuwa a Kano

KU KARANTA KUMA: Tsohon IGP Gambo Jimeta bai rasu ba – Iyalansa sun tabbatar

Sun kuma ce, rashin kofar na haifar da rudani ga baki wadanda ake wa kwatance da kofar a lokacin da za su shigo birnin na Kano domin harkokin kasuwanci da sauran harkoki.

A bangare guda munji cewa hawaye sun kwaranya yayinda aka sada Hajiya Zainab Murtala Nyako uwargidan tsohon gwamnan jihar Adamawa da gidanta na gaskiya.

Uwargidan tsohon gwamnan ta rasu ne a safiyar yau Laraba, 20 ga watan Yuni bayan tayi fama da yar gajeriyar rashin lafiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku neme mu a: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa ko Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng