Jigo a PDP ta koma APC da Dubunnan magoya bayanta

Jigo a PDP ta koma APC da Dubunnan magoya bayanta

- PDP na cikin matsalar sulalewar mambobinta zuwa jam'iyyar APC mai mulki

- Mutukar aka cigaba da haka to lallai akwai yiwuwar zaben 2019 zasu fsukanci gagarumar matsala

Wata jigo a jam’iyyar PDP a jihar Legas Remi Adiukwu ta sauya sheka zuwa jam’iyyar APC tare da dubunnan magoya bayanta a jiya Talata.

Jigo a PDP ta koma APC da Dubunnan magoya bayanta
Jigo a PDP ta koma APC da Dubunnan magoya bayanta

Adiukwu dai ta kasance tsohuwar kwamishina ce a jihar, bayan komawarta ta shaida cewa aiyukan da gwamnan jihar yake malalawa da kuma kyakyawan tsarin shugabacin APC ne suka ja ra’ayinta ta koma jam’iyyar.

A jawabinta yayin da ake karbarta Remi ta ce “Na dawo cikin jam’iyya, idan na ce da dawo to tabbas na dawo, zan bayar da gudunmaw ta dari bisa dari ‘’.

“Zabe na tahowa zamu yi duk mai yiwuwa iya karfinmu domin ganin mun tabbatar da jam’iyyarmu ta lashe duk kujerun muka bayar PDP ta same su a zaben 2015”.

“PDP yanzu ta mutu a wannan yankin, daga yanzu babu sauran adawa kowa yabi”

KU KARANTA: PDP ta tafka asarar dan majalisa zuwa APC a wata jiha

Da yake gabatar da nasa jawabin a yayin mika mata tuta a taron, shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Oshodi Alhaji Olamide Kasali cewa yayi, uwar jam’iyyar APC tayi maraba da dawowarta cikin jam’iyyar domin sun san irin yadda ta taimakawa PDP a zaben 2015.

Shi ma shugaban karamar hukumar Oshodi Bolaji Muse-Ariyo ya bayyana cewa cigaba da dawowar mutane cikin APC zai saukakawa APC a zabe mai zuwa 2019.

PDP dai na cigaba da fuskantar ficewar ‘yan jam’iyyar zuwa sauran jam’iyyu musamman ja’iyya mai mulki ta APC, inda ko a cikin satin nan ma a jihar Ekiti wani dan majalisa ya fice zuwa APC. Karanta cikakken labarin PDP ta tafka asarar dan majalisa zuwa APC a wata jiha

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel