Ka daina tafiye-tafiye marasa amfani – Sarki ga gwamnan jihar Zamfara

Ka daina tafiye-tafiye marasa amfani – Sarki ga gwamnan jihar Zamfara

Shugaban kungiyar jiga-jigan jihar Zamfara kuma sarkin Zamfra Anka, Alhaji Attahiru Ahmad ya bukaci gwamna Abdul-Aziz Yari da ya daina tafiye-tafiye marasa amfani a matsayin hanyar magance ayyukan ta’addanci a jihar.

Da yake Magana a fadarsa dake Anka, yayinda ya karbi bakuncin Gwamna Yari a ranar Sallah, basaraken yace irin wadannan tafiye-tafiye a kai a kai da gwamnan ke yi basu da amfani tunda jihar na fama da ayyukan ta’addanci.

A cewarsa, jihar Zamfara ce mazabar gwamnan don haka ya zama dole ya zauna ya taka rawarsa da kundin tsin mulki ta basa a matsayin gwamna.

“Tabbass mun san kaine shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, amma ka sani cewa, mutanen Zamfara ne suka zabe ka ba na Kano, Kaduna, Enugu ko wani jiha ba,” cewar sarkin.

Ka daina tafiye-tafiye marasa amfani – Sarki ga gwamnan jihar Zamfara
Ka daina tafiye-tafiye marasa amfani – Sarki ga gwamnan jihar Zamfara

Basaraken ya lura cewa yawan tafiye-tafiye da gwamnan ke yi akai-akai na haifar da yaya marasa idanu ga mutanen jihar musamman a yanzu da ake kisan kiyashi a kauyuka da biranen jihar.

Ya bayyana cewa kasancewar gwamnan a jihar zai taimaka matuka wajen lura da harkar tsaro a jihar.

KU KARANTA KUMA: Ekiti: Gangamin APC babu wani abun kirki sai borin kunya – PDP

Basaraken ya kuma ce ya zama dole gwamnati ta dauki kwakwaran mataki domin kawo karshen kashe-kashen ko kuma mutane su dauki mataki da kansu ta hanyar mallakar bindigogi domin su rama.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel