Jerin sunaye: Tsoffin gwamnonin Najeriya shida da aka yankewa hukunci bayan kama su da laifin aikata rashawa
Wani rahoto daga TransparencIT Nigeria ya lissafa shari’a shida da aka kammala na tsoffin gwamnonin da aka kama da rashawa.
An yankewa tsoffin shugabannin jihohin hukunci a kotunan Najeriya daban-daban bisa laifukan rashawa inda daya daga cikinsu da aka hukunta ya yi nasa zaman gidan yarin a kasar Amurka.
A cikinsu akwai tsoffin gwamnoni biyu da aka yankewa hukunci kwanan nan na jihohin Taraba da Plateau, Jolly Nyame da Joshua Dariye, sanata mai ci.
Wata babban kotun Abuja ta yankewa Nyame hukuncin shekaru 14 a gidan yari kan karkatar da Nnaira biliyan 1.64 , yayinda Dariye ma ya samu hukunci daurin shekaru 14 gidan yari bisa laifin almubazaranci da naira biliyan 1.16 na gwamnati yayinda yake shugabanci tsakanin 1999-2007.
Haka zalika wani tsohon gwamnan jihar Adamawa, wanda aka yankewa shekaru 5 a gidan yari ba tare da tara ba kan damfarar jiharsa naira miliyan 167.
Tsohon gwamnan jihar Edo, Lucky Igbinedion, ma ya samu hukuncin daurin watanni shida a gidan yari bisa zargin zambar kudi kimanin naira biliyan 25 amma ya samu yarjejeya da ya sa shi biyan tarar naira miliyan 3.5.
KU KARANTA KUMA: Jerin sunayen tsoffin gwamnoni 23 da adadin kudaden da ake zargin sun wawura
James Ibori na jihar Delta, wanda tuni ya kammala nasa zaman gidan yarin, wata kotun birnin Landan mai hukuncin daurin shekaru 13 a gidan yari bayan zambar dala miliyan 250, yayinda marigayi Diepreye Alamieyesegha na jihar Bayelsa ya sha daurin shekaru 2 a gidan yari bisa wata yarjejeniya bayan an kama shi da laifin zambar naira bilian 3.7.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Za ku iya samun mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng