Auren Soyayya na wasu ma’aurata yana tangal tangal saboda shan giya da rashin Sallah

Auren Soyayya na wasu ma’aurata yana tangal tangal saboda shan giya da rashin Sallah

Wata mata mai suna Hassana Angyan ta roki Kotu da ta raba aurenta da Mijinta, Shuabu Abdullahi sakamakon cikakken dan ruwa ne, wato mashayin giya, kuma baya gabatar da Sallah a matsayinsa na Musulmi, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Hassana ta bayyana haka ne a gaban Kotun Kubwa dake babban birnin tarayya Abuja a ranar Talata 19 ga watan Yuni, inda tace sun kwashe shekaru 30 sun aure da Abdullahi, kuma sun haifi yara shidda.

KU KARANTA: Marayu da yan gudun Hijira sun samu sabbin gidaje 200 daga hannun Dangote

Sai dai duk da dadewar da suka yi tare a matsayin miji da mata, Mijin nata baya sallah, babu abinda yake yi sai shaye shayen giya da kuma jibgarta kan duk wani da ya hada shi da ita, duk kankanci, kamar Allah ya aiko shi. Bugu da kari Uwargida Hassana tace ko Azumin Ramadan da ya wuce Abdullahi bai yi ba.

Da wannan ne Uwargida ta roki Kotu ta kawo karshen wahalhalun da take fama da shi a gidan Abdullahi, kan laifukan da take zarginsa da su da suka kunshi shan giya, kin sallah da kuma dukanta akai akai.

Sai dai a nasa jawabin, Abdullahi ya amsa dukkanin laifukan da Hassana ke tuhumarsa dasu, inda ya roki Kotu da cewa kada a raba auren nasa, ya ruba ba zai kara shan giya ba, kuma zai dinga raba albashinsa gida biyu yana bata rabi.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu ne, sai Alkalin Kotun, Mai shari’a Abdulwahab Mohammed ya roki Hassana ta yi hakuri, ta cigaba da lura da halayen Abdullahi tun ya tuba, ta kawo masa rahoto zuwa ranar 28 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel