Yadda Gawar wata Mata ta hallaka Dan cikinta a yayin da ake tsaka da jana’iza

Yadda Gawar wata Mata ta hallaka Dan cikinta a yayin da ake tsaka da jana’iza

Tabbas idan ajali yayi kira ko ba ciwo sai an je, kwatankwacin wannan ne ya faru ne a kasar Indonesia, inda a yayin da ake tsaka da jana’izar wata Mata, kwatsam sai gawarta ta fado a cikin akwatin gawa, ta murkushe shi, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya faru ne a unguwar Sulawesi dake yankin Arewacin lardin Toraja na kasar, a ranar Juma’a na watan Yuni, a lokacin da akwatin dake dauke da gawar Matar ke kwance akan wani dandamali.

KU KARANTA: Wani matashi ya sake kashe kansa a masallacin Makkah

Yadda Gawar wata Mata ta hallaka Dan cikinta a yayin da ake tsaka da jana’iza
Smen Kondura

Sai dai abinka da tsautsayi, yaron mata mai shekaru 40, Smen Kondura ya tashi ya kusanci gawar mahaifiyar tasa, bayan ta fara faduwa daga hannun masu daukar gawa, daga nan sai aka daura ta akan dandamalin, amma ta kaar faduwa, wannan karon akan yaronta, inda ya fadi matacce nan take.

Kwamishinan Yansandan yankin, Julianto Sirat ya bayyana cewa bayan ga kashe mutumin, gawar mahaifiyar tasa ya jikkata mutane da dama daga cikin wadanda suka halarci jana’izar tata.

Yadda Gawar wata Mata ta hallaka Dan cikinta a yayin da ake tsaka da jana’iza
Hatsarin

Sai dai kwamishinan ya danganta faruwar wannan mummunan lamari ga rashin daidaita wani kwaranga dake dauke da nauyin gawar, sai dai iyalan matar sun ce ba zasu kai karar kowa ba, ind tuni aka binne Smen tare da mahaifiyarsa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel