A wata balahira, an kona gidaje 15 tare da kashe wani mai Sarautar gargajiya
- A rashin sa'a, wata hatsaniya tayi sanadiyyar shekawar wani mai sarautar barzahu
- Dama kafin wannan rikici rahotanni sun nuna ta ciki na ciki tsakanin mai sarautar da wasu mutane
Wasu wadanda ba a san ko su wane ba sun hallaka Igwe Nwatu har lahira. Nwatu dai shugaba ne mai rike da sarautar gargajiya a garin Ogbozine Akpugo dake yammacin karamar hukumar Nkwau a jihar Enugu.
Majiyar ‘yan sanda ta bayyanawa cewa Nwatu an kashe shi ne yayin dawo gida daga halartar wani zama da ya yi a wata kotun dake karamar hukumar Nkanu West.
Mamacin dai ya halarci kotun ne bisa rakiyar ‘yan sanda guda hudu wanda suke tsaronsa har bayan an tashi daga zaman kotun suna biye da shi.
Wadanda suka kai farmakin sai da suka raba yan sandan da makamansu sannan suka shiga dukan Nwatu kafin daga bisani ne jami'an yan sanda suka samu bayani, nan take suka garzaya da shi zuwa asibiti inda aka fara masa rigakafi kafin kuma su dauke shi zuwa babban asibitin cikin garin Enugu ne ya rasu da misalin karfe 9:00pm na dare.
KU KARANTA: Ba ni kadai ba ne barawo a Najeriya, yan siyasa ne manyan barayi amma ba’a musu komai – Barawon Keke Napep
Mamacin dai ya yi ƙaurin suna wajen cuzgunawa mutane dake ƙarƙashinsa, wanda a ko da yaushe ba abinda suke face korafi akansa musamman wajen aikata munanan abubuwa akansu.
A bisa binciken da ‘yan sanda suka gudanar an samu harsashi daya wanda na daya daga cikin jami'an yan sandan dake tsaron mamacin ne, har wa yau, iyalansa sun bayyanawa cewa ya rasu ne bisa raunukan da ya samu a jikinsa.
A yanzu haka dai sama da gidaje 15 ne aka kona wanda hakan ya samo asali daga rikicin da masu goyon bayan mamacin suka tayar, sun aikata hakan ne kuma akan duk wanda suka san suna zaman adawa da mamacin, inda suka kone duk wani gida da kuma dukiyoyinsa.
Mai magana da yawun hukumar ‘yan sanda ta jihar Ebere Amaraizu ya tabbatar da Jaridar vanguard rasuwar Nwatu ta hanyar sakon kar ta kwana. Yanzu haka hukumar tasu tana cigaba da gudanar da bincike domin gano duk wani wanda ke da hannu a cikin wannan mummuna aiki da aka aikata.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng