Wata fusatacciyar karuwa ta yayyagawa wani ‘dan sanda kaya sannan ta galla masa cizo

Wata fusatacciyar karuwa ta yayyagawa wani ‘dan sanda kaya sannan ta galla masa cizo

- Idon wata budurwa mai zaman kanta ya raina fata a dalilin rigima da jami'an tsaro

- Yanzu haka an damke har an gurfanar da ita gaban kuliya

- Nan take shi kuma alkalin ya yanka mata bizar zuwa gidan yari

Wata kotun majistirie ta umarci da a tisa ƙeyar wata matashiyar karuwa mai shekaru 25 da haihuwa zuwa gidan kasa, karuwar mai suna Chizoba Ajukwu ana tuhumar ta ne da yin fada da wasu jami'an ‘yan sanda har mutum biyu a garin na Isolo na jihar Legas

Wata fusatacciyar Karuwa ta yayyagawa wani ‘Dan sanda kaya sannan ta galla masa cizo
Wata fusatacciyar Karuwa ta yayyagawa wani ‘Dan sanda kaya sannan ta galla masa cizo

Wadda ake tuhumar, wadda jami'an yan sandan suka bayyana a matsayin karuwa sun ce ta takale su da fada ne saboda sun yi kokarin kama ta.

‘Yan sandan sun bayyanawa kotun cewa, yarinyar ta yaga kakin guda daga cikinsu inda kuma ta ciji dayan a lebbansa a lokacin da yayi yunkurin sanya ta a cikin motarsu ta farautar masu laifi.

Sun ce sai da suka hadu har su uku a sannan ne suka samu damar kama ta har suka kaita ofishinsu, wanda daga nan ne aka gurfanar da ita a kotun majistiri ta Isolo wanda kotun kuma ta bada umarnin a tsare ta a gidan kaso.

KU KARANTA: Idon wasu ƴan sanda ya raina fata bayan an kama su suna aikata wani abu, karanta kaji

Wannan al'amari ya faru ne a Otel din Okota dake jihar Legas, wanda a nan ne wannan matashiya ke yin sana'arta ta karuwanci.

‘Dan sanda mai gabatar da kara ya bayyana Kotun cewa, matashiyar ta samu saɓani ne da wata abokiyar sana'arta wanda har ta kai ga ta dauko reza tana mata barazana da ita. An yi kokarin ganin an kawo karshen rikicin amma abin ya ci tura wanda daga nan ne aka bugawa jami'an yan sanda waya, suka zo suka kama ta.

Alkalin kotun ta bada belin ta akan kudi Naira dubu 100,000 bisa sharadin kawo wanda zai tsaya mata, amma kafin lokacin, alkalin ta tisa keyarta zuwa gidan kaso har sai ta cika wadannan sharuda sannan za a sake ta.

Kana daga bisani ta ɗage karar zuwa 26 ga watan Yuli na shekara ta 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel