Gari ban-ban: Ku kalli hotunan wata dabbar ruwa mai ban mamaki da ruwan teku ya kawo ban kasa

Gari ban-ban: Ku kalli hotunan wata dabbar ruwa mai ban mamaki da ruwan teku ya kawo ban kasa

Jama'ar wani gari dake a wurin shakatawar gefen teku a kasar Namibia sun shiga rudani da al'ajabi biyo bayan ruwa ya fiddo wata matattar dabbar ruwa mai ban al'ajabi da ke da tsawon kusan kafa 20.

Jim kadan da faruwar hakan kuwa sai masana kimiyya a kasar suka bazama suna son su gano ko wace irin dabba ce kuma meye dalilin mutuwar ta.

Gari ban-ban: Ku kalli hotunan wata dabbar ruwa mai ban mamaki da ruwan teku ya kawo ban kasa
Gari ban-ban: Ku kalli hotunan wata dabbar ruwa mai ban mamaki da ruwan teku ya kawo ban kasa

KU KARANTA: Bidiyon wani faston da ya musulunta a jihar Ebonyi

NAJI.com ta samu cewa sakamakon binciken farko-farko dai da suka fara fitarwa ya nuna cewa dabbar nau'i ne kifaye 'yan ajin dorinar ruwa kuma sunan ta na kimiyya shine Ziphius cavirostris sannan tana rayuwa ne a can kasan teku kuma kashin kumatun ta ne ya kare wanda suka zargi shine yayi sanadiyyar ajalin dabbar.

Haka zalika masanan sun bayyana cewa duk da cewar ba kasafai ake ganin kifayen ba, amma ana kiyasta cewa sun kai guda dubu 100 a dukkan tekunan duniya.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng