Chelsea na fuskantar barazanar sayarwa, har an taya €21b

Chelsea na fuskantar barazanar sayarwa, har an taya €21b

- Fargaba ta mamaye zukatan magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, tun bayan da aka ki sabuntawa mamallakin kungiyar Fasfonsa

- Dadin da dawa kuma aka hana shi shiga kallon wasan karshe na kofin FA kungiyar da ta buga da Manchester United

Biyo bayan rashin tabbas ga makomar mamallakin ƙungiyar ƙwallon kafa ta Chelsea ɗan asalin kasar Rasha Roman Abramovich a ƙasar Ingila, yanzu haka shahararren mai kuɗin nan na ƙasar ta Ingila Jim Ratcliffe ya taya Chelsea zunzurutun kuɗi har £21b.

Tun dai hawan sabuwar Firaministar ƙasar Theresa May dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashen biyu, wanda hakan ke barazanar cigaba da zaman Abramovich ɗin cikin Ingilan sakamakon wahalar sabunta Fasfo ɗinsa.

Ko za'a siyar: An taya Chelse kuɗin yanke Talauci har €21b
Roman Abramovich

An dai rawaito cewa mamallakin Chelsea ya hasala matuƙa bisa hana shi shiga kallon wasan ƙarshe na cin kofin FA da Chelsea ta buga ranar 19 ga watan Mayu inda daga bisa cikin kwanaki ƙalilan ya nemi takardar zama ɗan ƙasar Isra'ila kuma aka ba shi ba tare da ja'in ja ba.

KU KARANTA: Dubban mutane sun nemi a hukunta Sergio Ramos kan Mo Salah Matuƙar dai ba'a sabuntawa Abramovich Fasfon na shi ba, to ba zai samu damar gudanar aiki a ƙasar ba duk kuwa da cewa yana da damar shigowa ƙasar har na tsawon watanni shida ta hanyar amfani da sabon Fasfon da Isra'ila ta bashi.

An dai ƙiyasta darajar kuɗin mai shirin siyan Chelsea zai kai har £45bn kamar yadda yazo na ɗaya a jadawalin Sunday Times. Yana da mutane 18,500 a ƙasashen 22 da suke masa aiki.

Ko za'a siyar: An taya Chelse kuɗin yanke Talauci har £21b
Jim Ratcliffe

Shi dai Mr Ratcliffe magoyin bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ne sosai domin har gida yake da shi a kusa da filin wasa na ƙungiyar. Sai dai kuma wasu rahotannin sun bayyana cewa Abramovich ɗin ya ƙi amincewa da tayin, domin a shirye yake da ya cigaba da riƙe ƙungiyar.

Abramovich ya sayi ƙungiyar ta Chelsea ne a shekara ta 2003 kan kuɗi £140m.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel