Kasar Austria ta shirya rufe masallatai 7 tare da korar limamai da dama daga kasar

Kasar Austria ta shirya rufe masallatai 7 tare da korar limamai da dama daga kasar

Kasar Austria dake a yammacin duniya ta sanar da kudurin ta na rufe wasu masallatai har bakwai da tace tana zargin suna karbar kudaden gudanarwar su daga kasashen waje tare kuma da korari wasu limaman masallatan kasar da dama.

Shugaban kasar ta Austria ne dai mai suna Sebastian Kurz ya sanar da kudurin gwamnatin da yake jagoranta a ranar Juma'ar da ta gabata inda ya kara da cewa za su dauki matakin ne domin tsarkake harkokin addinai a kasar.

Kasar Austria ta shirya rufe masallatai 7 tare da korar limamai da dama daga kasar
Kasar Austria ta shirya rufe masallatai 7 tare da korar limamai da dama daga kasar

KU KARANTA: Bama-baman 'yan Shi'a sun fashe a masallaci

Legit.ng ta samu cewa dalilin da ya ja gwamnatin kasar daukar matakin dai shine na yadda wasu masallatan kasar ke kokarin saka siyasa da kuma tayar da tarzoma a tsakanin 'yan kasar ta hanyar tunatar da su wasu abubuwan da suka auku na tarihi a shekarun baya.

A wani labarin kuma, Biyo bayan matakan da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta dauka na kara haraji a kan giya da taba a kasar nan tun daga ranar 1 ga watan Yunin da ta gabata, hakan ya tilastawa kamfanonin da ke sayar da kayayyakin kara farashin shu da akalla kaso 15 cikin 100.

Wannan ne ma ya sa shugaban wani kamfanin dake sayar da giya a garin Legas da ya bukaci a sakaya sunan sa ya bayyana cewa tuni kamfanin su yayi kwaskwarima a farashin giyar su inda kiret yanzu ya koma Naira dubu 3 da dari biyar sabanin Naira dubu 3 da yake a da.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng