Jami'an kwastam sun kafa tarihi, sun yi abun da basu taba yi ba a Najeriya

Jami'an kwastam sun kafa tarihi, sun yi abun da basu taba yi ba a Najeriya

Jami'an hana fasa kwauri na Najeriya da aka fi sani da kwastam watau Nigeria Customs Service (NCS) a turance sun kafa tarihi, yayin da suka tara kudaden da ba'a taba tarama gwamnatin tarayya ba a wata daya na Naira biliyan 100.1 a watan Mayun da ya gabata.

Ganin namijin kokarin da suka yi ne ma kuma ya sa jami'an suka kara mika kokon barar su ga gwamnatin tarayya da ta duba girman Allah ta kara masu albashi.

Jami'an kwastam sun kafa tarihi, sun yi abun da basu taba yi ba a Najeriya
Jami'an kwastam sun kafa tarihi, sun yi abun da basu taba yi ba a Najeriya

KU KARANTA: An sanar da rufe majalisar tarayya

Legit.ng dai ta samu cewa dukkan wannan bayanan sun fito ne daga bakin shugaban hukumar na kasa, Kanal Hameed Ali mai ritaya yayin da yake jawabi wajen bukin yaye wasu manyan jami'an hukumar da suka yi wani kwas don habaka yanayin aikin su a garin Abuja.

A wani labarin kuma, Yanzu haka dai ana zaman dar-dar ne a hukumar nan dake da alhakin gudanar da zabukan kasa ta tarayyar Najeriya watau Independent National Electoral Commission (INEC) sakamakon wata cakwakiya da ta ke neman kunno kai.

Kamar dai yadda muka samu, wata kotun tarayya ce a baya ta bayar da umurni ga bankunan kasar nan da su daskarar da makudan kudaden hukumar da suka kai akalla Naira biliyan 34 dake cikin asusun ta.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel