Sabuwar ranar Dimukuradiyya: Su wa da wa ya kamata ku san rawar da suka taka a zaben 12 ga watan Yuni 1993
- Shekaru 25 bayan soke zaben 12 ga watan Yuli (1993) Gwamnatin Najeriya ta girmama Chief Moshood Abiola da lambar girmamawa ta GCFR
- Abiola na jam’iyyar SDP shi ne dai aka hakikance ya lashe zaben da suka kara da Bashir Tofa daga jam’iyyar NRC
- Zaben dai na 12 ga watan Yuni 1993 shi ne wanda yafi kowanne zabe tsafa da rashin magudi a tarihin Najeriya
Shekaru 25 bayan da Gwamnatin Soja ta wancan lokaci karkashin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta soke zaben da a aka hakikance Moshood Abiola ne ya samu nasara, yau Legit.ng ta yi duba ne izuwa wasu Mutane 11 da suka taka rawar gani da ya kamata ku sani.
Marigayi Moshood Abiola
Zaben dai kamar yadda aka sha fada Marigayi Moshood Abiola ne wanda ake yiwa lakabi da MKO ya samu rinjaye, kuma yana daya daga cikin batun siyasar da yayi shura a kasar nan wanda har yanzu ake maganarsa.
Kuma yayi takara ne a karkashin jam’iyyar SDP (Social Democratic Party), yayinda abokin karawar tasa Bashir Tofa ya fito daga jam’iyyar NRC (National Republican Convention).
KU KARANTA: Ranar 12 ga watan Yuni: Yadda IBB ya soke zaben shugaban kasa na MKO Abiola a shekarar 1993
Zaben dai Gwamnatin mulkin soja ta lokacin wadda Janar Ibrahim Babaginda ke jagoranta ce ta soke shi, wanda a sakamakon hakan ya fuskanci suka daga Mutane da yawan gaske ta ko’ina, har hakan ta sanya ya sauka ya nada Gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin Ernest Shonekan.
Ibrahim Babaginda
Amma sai dai wani abin mamaki da ba kowa ne ya sani ba shi ne, Moshood Abiola da shugaban kasa na lokacin Babaginda manyan abokai ne na kut da kut.
Yanzu haka dai shi tsohon shugaban kasa Ibrahim Babaginda ya kasance mamba ne a jam’iyyar PDP, kuma ya sha yunkurin ganin sake darewa shugabancin kasar nan a matsayin farar hula, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba, domin ya gaza koda samun tikitin yiwa jam’iyyar takara ko sau daya.
Wani abu kuma da yake daurewa Mutane kai shi ne yadda Babangidan ya kasa bayar da tartibiyar amsa gasasshiya kan dalilin da ya sanya ya soke zaben, abinda wasu ke ganin kawai bai shirya mika mulki ba ne a lokacin.
Amma duk da cewa shi ne aka hakikance ya lashe zaben, Moshood Abiola ya tsinci kanshi ne a garkame bayan da Janar Sani Abacha ya hau karagar mulki, sakamakon bayyanawa karara da yayi cewa shi ya ci zaben 12 ga watan Yuni ba tare da jiran hukuma ta ayyana shi ba.
Humphrey Nwosu
Humphrey shi ne shugaban hukumar zabe a wancan lokacin da ake kira da NEC (National electoral commission) da ta gudanar da tsaftataccen zaben cikin karbabben yanayi maras magudi.
Gabannin zaben (1993) hukumar ta bijiro da wasu tsare-tsare da suka kawo sauyi a harkokin gudanar da zabe, kamar tsarin zabe na A4 da bullo da takardar kada kuri’a da kuma tanadar Mutane har 3,000 da zasu sanya ido kan zaben a kasa baki daya. Wanda hakan ya kasance sabanin yadda ake yin zabe a baya.
Marigayi Janar Sani Abacha
Ta karfin tsiya bisa tilastawa ya saukar da shugaban rikon kwarya Ernest Shonekan da Janar Babangida ya dora watanni uku kacal da hawansa.
Gwamnatinsa dai tayi kaurin suna wajen kulle bakin ‘yan adawa ta hanyar sanya su a magarkama, hakan ta sanya ‘yan adawar fecewa zuwa wasu kasashen domin neman mafaka, yayinda wasu kuma suka kakkafa kungiyoyi domin adawa da shi.
Haka zalika Abacha ne ya sanya aka damko Abiola bayan da ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben 1993, hakan kuma laifi ne na cin amanar kasa inji Gwamnatin Abachan. Abiola dai har ya gamu da ajalinsa yana tsare ne ba tare da an sake shi ba.
Alhaji Bashir Tofa
Shi ne abokin karawar Abiola kuma wanda yayi masa mataimaki shi ne tsohon Gwamnan babban bankin Biafra Sylvester Ugoh.
Bashir Tofa daga baya ya koma cikin sabuwar jam’iyyar APC wadda ke mulki a halin yanzu, kuma yana cikin ‘yan kwamitin amintattu na jam’iyyar.
Arthur Nzeribe
Wani dan gani kashen shugaban mulkin Soja na wancan lokacin wanda tun kwanaki biyu gabanin zaben (10/06/1993) yayi yunkurin dakatar da shi baki daya karkashi wata kungiya da yake jagoranta mai suna ABN (Association for Better Nigeria) bisa dogaro da wata takardar izini da ya samo daga wata babbar Kotu a Abuja daga mai shari’a Bassey Ikpeme.
Babagana Kingibe
Ba kowa ne ya san wanene mataimakin dan takarar shugabancin kasa Abiola a zaben 12 ga watan Yuni, amma tarihi ba zai manta da cewar Babagana Kingibe shi ne abokin takarar Abiolan a matsayin mataimakinsa ba, wannan dai shi ne karon farko da aka taba samun yan takarar shugabancin kasa da mataimakinsa dukkansu Musulmai.
Ndubisi Kanu
An ba shi mukamin Gwamna a jihar Imo a shekarar 1976 amma daga baya ya tsunduma siyasa har ma ya bayar da gagarumar gudunmuwa da ta kai ga shirya zaben 1993, Kuma shi neya shugabanci NADECO.
Amma duk da cewa yana cikin Gwamnatin Babangida hakan bai hana shi sukarta ba yayin da ya fuskanci ta fara kaucewa hanya.
Doyin Okupe
Okupe jigo ne a jam’iyyar NRC a shekarar 1993 kuma rahotanni sun bayyana cewa har ya yiwa ‘yan jam’iyyar SDP murnar nasararsu a zaben amma kwatsam sai labari ya canja inda aka ji daga bisani ya fadawa ‘yan Najeriya cewa Babangida ne ya shaidawa Tofa kada ya yarda an kada shi.
Okupe ya rike mukamai a Gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da kuma Goodluck Jonathan.
Tom Ikimi
Shi ne shugaban jam’iyyar NRC na wancan lokacin kuma kamar yadda Tofa yaki amincewa da zaben haka shi ma yayi watsi da shi, har ma a maganarsa yake nuna goyo bayan soke zaben da aka yi.
Tom Ikimi daga baya ya rike mukamin Ministan harkokin waje a Gwamnatin Janar Sani Abacha kuma ya daga cikin wadanda suka yi nakudar jam’iyya mai mulki a yanzu (APC) amma sai dai yayi rashin nasara a takarar zama shugabanta da yayi.
Tony Anenih
Anenih ya bayar da gudunmuwa sosai wanda hakan ya kai ga irin karbuwar da jam’iyyarsu ta SDP ta samu har ta taka rawar gani a zaben 1993 din, amma sai dai bayan soke zaben ya fito fili inda ya bayyana cewa ya rungumi kaddarar soken zaben a Gwamnati mai ci ta yi, wanda hakan ya janyo masa suka mai tarin yawa.
Tony Anenih jigo ne a jam’iyyar PDP kuma har ma ya rike mukamin Ministan aiyuka a baya.
Yanzu haka dai shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar da sauya ranar murnar Dimukuradiyya ta kasa daga ranar 1 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni, Sannan ya kuma sanar da bayar da lambar girmamawa mafi kololuwar daraja a Najeriya ta GCFR ga wanda aka hakikance samun nasararsa a zaben wato Moshood Abiola.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng