Majalisar dokoki na siyasar yunwa – Jigon Auchi

Majalisar dokoki na siyasar yunwa – Jigon Auchi

Wani jigo a masarautar Auchi, Alhaji Usman Abudah, Dan’iyan Auchi a jihar Edo, ya bayyana barazanar da majalisar dokoki tayi na tsige shugaban kasa a ranar Talata a matsayin “siyasar yunwa”.

Abudah yace barazanar nuni ga wakilcin lalaci ga al’umman Najeriya.

Ya fadawa manema labarai a birnin Benin cewa hallayar yan majalisar wajen siyan jirgin yakin Tucano 12 domin yaki da ta’addanci ya nuna cewa yan majalisan basu damu da jin dadin yan Najeriya ba.

A cewarsa, “Shugaban kasar na kula da dukkanin hukumomin tsaro dake yaki day an ta’addan Boko Haram sannan kuma ana samar da makaman da ake bukata.

Majalisar dokoki na siyasar yunwa – Jigon Auchi
Majalisar dokoki na siyasar yunwa – Jigon Auchi

"Mutum ya ma rasa mai yan majalisan ke son shugaban kasar yayi. Shin so suke yi yaje ya kwashi kayansa na sojoji ya je yaki?”.

KU KARANTA KUMA: Matakan tsige shugaban kasa 8 a kundin tsarin mulkin Najeriya

Ya kalubalanci yan majalisan kan su san abunda ya kamace su.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa a ranar Talata, 5 ga watan Yuni yan majalisa sun ja kunnen shugaban kasa Muhammadu Buhari kan ya bi sharudansu ko su dauki mataki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Domin samun ingantattun labaranmu bide mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel